Noma tushen arziki: FG ta samar wa matasa 130,000 aikin yi

Noma tushen arziki: FG ta samar wa matasa 130,000 aikin yi

Audu Ogbeh, Ministan Noma da Raya Karkara, ya ce gwamnati da dauki matasa 130,000 aiki a matsayin malaman gona a sassan Najeriya daban-daban.

Ministan ya bayyana hakan ne a wurin taron shekara-shekara karo na 24 na Kungiyar Malaman Gona ta Najeriya (AESON) ta aka gudanar ranar Litinin a babban birnin tarayya, Abuja.

Ogbeh wanda ya samu wakilcin Karima Babangida ya ce an bawa matasan aiki ne karkashin shirin samar da ayyukan yi ga matasa na kasa na gwamnatin tarayya wato NSIP.

A cewarsa, akwai bukatar a inganta ayyukan malaman noma domin samun cigaban da ake bukata a yunkurin da gwamnati ke yi na farfado da bangaren noma.

DUBA WANNAN: Saurayi ya kashe wacce zai aura saboda ta raina girman mazakutarsa

Noma tushen arziki: FG ta samar da aikin yi fa matasa 130,000
Noma tushen arziki: FG ta samar da aikin yi fa matasa 130,000
Asali: Twitter

Ya ce an bawa matasan horo kuma nan ba da dadewa ba za a basu na'ura mai kwakwalta ta hannu domin tallafa musu wurin gudanar da ayyukansu kamar yadda ya dace.

"Malaman aikin noma suna ta muhimmiyar rawa da za su taka wurin farfado da bangaren noma a kasar nan," inji shi.

"Najeriya tana da duk abinda ake bukata na bunkasa a fanin noma.

"Baya ga noma, an kuma bawa sauran masu harkar noma tallafin kayan aiki domin su inganta aikinsu su karawa kayansu daraja.

"Akwai bukatar a kara wa manoma ilimi domin inganta ayyukansu saboda hakan zai kara darajar kayayakin noma a kasar.

"Wannan shi yasa ake bukatar malaman aikin noma saboda su tallafawa manoma inganta ayyukansu da kara samun amfanin gona mai yawa."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel