Ya aka yi APC ta rasa Bauchi, Adamawa, Benue, Imo, Sokoto da Oyo

Ya aka yi APC ta rasa Bauchi, Adamawa, Benue, Imo, Sokoto da Oyo

Yanzu haka dai an yi zaben 2019 an gama, inda manyan jam’iyyun Najeriya na APC da kuma PDP su ka gamu da nasara da kuma rashin ta. Daga cikin zabukan da su kayi fice su ne na jihar Sokoto, Kano, Bauchi, Adamawa da sauran su.

Daily Trust ta kawo rahoto a kan yadda APC ta rasa Imo, Oyo da sauran jihohin ta, yayin da PDP mai adawa ta gaza cigaba da rike jihohin Gombe da kuma Kwara, inda nufin gwamnonin na nada Magadan su a PDP ya gaza kai ga ci.

1. Nasarar Ortom a Benuwai

Ta tabbata cewa APC ta rasa jihar Benuwai bayan Samuel Ortom ya samu zarcewa a kan kujerar gwamna. Ortom ya bar APC ne kwanaki inda ya sauya-sheka zuwa PDP. Gwamnan ya tsallake barazanar Majalisa har ya samu tikiti a PDP.

Samuel Ortom yayi gumurzu ne da Sanata George Akume har ya kai ga samun nasara. Manyan ‘Yan siyasa irin su David Mark, Gabriel Suswam, Abba Moro, da Iyorchia Ayu, da kuma John Ngbede sun taimakawa Gwamnan a zaben 2019.

2. Sokoto ta koma hannun Jam’iyyar adawa

Jihar Sokoto ta koma hannun jam’iyyar adawa kamar yadda aka san ta tun a 1999. Gwamna Aminu Tambuwal yana cikin gwamnonin da su ka bar APC zuwa PDP a bara. Tambuwal ya kuma samu nasarar doke APC da kuri’a 300 a zaben bana.

3. PDP ta ci banza a Jihar Imo saboda rikicin APC

Emeka Ihedioha ne ya amfana da rikicin da ake ta faman yi tsakanin jam’iyyar APC mai mulkin jihar da kuma AA wanda Rochas Okorocha ya tsaida Surukin sa Uche Nwosu. Wannan rikici na Okorocha da APC ya sa Hope Uzodinma ya sha kashi.

KU KARANTA: Sanata Adeleke ya sake samun nasara wajen takarar Gwamnan Osun

4. Jihar Kwara ta dawo hannun Jam’iyyar

Tun fil azal Jihar Kwara ta ke hannun jam’iyya mai mulki kafin Bukola Saraki ya sauya-sheka zuwa APC a 2013. A bara ne kuma Shugaban majalisar dattawan da gwamna Abdulfattah Ahmed su ka dawo PDP inda su ka sha mugun kashi a zaben bana.

5. Gwamna Ajimobi ya mikawa PDP mulki

Irin salon mulkin Gwamna Abiola Ajimobi ne ya jawo PDP ta karbe mulki a jihar Oyo ta hannun Seyi Makinde da kuri’a fiye da 150, 000. Gwamnatin APC ta samu rashin farin jini wajen Malaman addini da kuma ‘Yan makaranta a jihar Oyo.

6. APC ta karbe ragamar Jihar Gombe

Tun 2003 ne jam’iyyar PDP ta karbi mulki a jihar Gombe bayan da Muhammad Danjuma Goje ya doke Abubakar Habu Hashidu na ANPP. A zaben bana, Muhammad Inuwa Yahaya, ya doke Usman Bayero Nafada na PDP war-was a zaben.

7. PDP ta karbe mulkin Jihar Bauchi

‘Dan takarar Jam’iyyar PDP watau Bala Mohammed ya tika gwamna Mohammed Abubakar da kasa a zaben na 2019. Bayan irin rawar gwamnatin APC a jihar, PDP mai Yakubu Dogara, Sulaiman Nazif da Isah Hamma Misau ‎sun yi wa APC taron-dangi

8. PDP ta ci bulus a rikicin Jihar Adamawa

Atiku Abubakar da Ahmadu Fintri sun samu nasara a jihar Adamawa a dalilin rikicin cikin-gidan da ya ci APC. Gwamna Bindow ya samu sabani da manyan APC irin su Babachir Lawan, Abubakar Gire, Bello Tukur, Buba Marwa, Musa Kamale, Nuhu Ribadu, Mahmud Halilu, har da kuma Mai dakin Shugaban kasa Aisha Buhari.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel