Kannywood: Nafisa Abdullahi ta soki Buhari a kan kashe-kashen Zamfara

Kannywood: Nafisa Abdullahi ta soki Buhari a kan kashe-kashen Zamfara

- Jarumar Kannywood, Nafisa Abdullahi ta nuna bacin ranta kan yadda shugaba Buhari ya ke fifita matsalolin kudu a kan na Arewa

- Jarumar tayi wannan korafin ne a lokacin da Shugaba Buhari ya yi magana a kan kisar wani matashi a Legas mai suna Kolade Johnson da yan sanda suka kashe

- Nafisa Abdullahi ta ce shugaba Buhari baya nuna damuwarsa a kan kashe-kashen Zamfara da sauran jihohin Arewa amma idan abinda ya shafi 'yan kudu ne yana bashi muhimmanci

Kannywood: Jaruma Nafisa tayi kaca-kaca da Buhari a kan kashe-kashen Zamfara
Kannywood: Jaruma Nafisa tayi kaca-kaca da Buhari a kan kashe-kashen Zamfara
Asali: Twitter

Fitacciyar jaruman Kannywood, Nafisa Abdullahi tayi kaca-kaca da shugaban kasa Muhammadu Buhari a kan rashin cewa komai a kan kashe-kashen da akeyi a wasu kauyukan jihohin Zamfara.

Jarumar ta soki shugaba Buhari a bisa maganan da ya yi a kan kisar wani matashi, Kolade Johnson da wasu 'yan sanda biyu suka kashe a Legas amma bai ce uffan ba a kan kisan kiyashin da 'yan bindiga su ke yiwa al'umma a Zamfara.

DUBA WANNAN: Yadda PDP ke kokarin hana Lawan zama shugaban majalisar dattawa - Majiyar APC

"An kashe daruruwa ko dubban mutane a Zamfara da wasu sassan Arewa kafin kisar Kolade amma ba ka yi magana a kai ba ... ina tsamanin kana tsaron yin maganar ne amma tunda wannan a kudu ya faru, tuni har kayi magana a kai." Kamar yadda Nafisa ta rubuta a Twitter.

Nafisa tayi rantsuwa cewa al'ummar Najeriya ne suke janyo matsalar da ake fama dashi a kasar, "Ana kashe mutanen ka a kasarka. Ba za kayi magana a kansa ba amma ka na nuna alhinin ka bisa rasuwar wani da ke wata bangare na duniya da bai damu da kai ba kuma watakila baya bukatar "

Jarumar ta ce ba ta fatan a rika kashe wasu mutanen, "amma abin lura a anan shine, ko sun damu da halin da ka ke ciki da matsalolin da ke damun ka? Ko sun san kana rayuwa ma?

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel