'Yan sanda sun kama mai kera wa da safarar bindigu a Sokoto

'Yan sanda sun kama mai kera wa da safarar bindigu a Sokoto

- Kakain rundunar 'yan sanda a jihar Sokoto ya tabbatar da kama wani mutum dake safara da kera bindigu

- An kama mutumin mai suna Ibrahim Alhassan a kauyen Runbukawa dake jamhuriyar Nijar mai makwabtaka da jihar Sokoto

- Kwamishinan 'yan sanda a jihar Sokoto, Mista Ibrahim Kaoje, ya bayar da umarnin gudanar da atisaye a dukkan sassan jihar domin tabbatar da tsaron lafiyar jama'a da dukioyoyinsu

Rundunar 'yan sanda ajihar Sokoto ta sanar da kama wani mutum mai suna Ibrahim Alhassan, wanda aka samu da bindigu biyu kirar hannu da zagaye 18 na alburushi

Kakakin rundunar 'yan sanda a jihar Sokoto, ASP Muhammad Sadiq, ya tabbatar da kama mutumin yayin gabatar da jawabi ga manema labarai a Sokoto.

Sadiq ya ce: "wata tawagar jami'an 'yan sanda a ofishinmu na karamar hukumar Sabon Birni ta kama wani mutum mai suna Alhassan a kauyen Runbukawa dake jamhuriyar Nijar ranar Talata.

"An same shi da bindigu biyu kirar gida da zagaye 18 na alburusai, ya amsa da bakinsa cewar ya sayar da wasu bindigu biyu a kauyen Mailalle dake karamar hukumar Sabon Birni a kan farashin N10,000 kowacce daya.

'Yan sanda sun kama mai kera wa da safarar bindigu a Sokoto

Jami'an 'yan sanda
Source: Twitter

"Sannan ya masa da bakinsa cewar shine yake kera bindigun," a cewar kakakin na rundunar 'yan sanda.

DUBA WANNAN: Rashin tsaro: Kotun sauraron korafin zabe ta canja matsuguni daga Zamfara

Ya kara da cewa an kama mutumin ne biyo bayan kara matsin lamba da jami'an 'yan suka yi wajen kakkabe 'yan ta'dda da rage aiyukan ta'addanci a jihar Sokoto.

Ya ce kwamishinan 'yan sanda a jihar Sokoto, Mista Ibrahim Kaoje, ya bayar da umarnin gudanar da atisaye a dukkan sassan jihar domin tabbatar da tsaron lafiyar jama'a da dukioyoyinsu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel