Jerin sunayen sojojin Najeriya da ISWA ta hallaka

Jerin sunayen sojojin Najeriya da ISWA ta hallaka

An bayyana sunayen dakarun sojojin Najeriya biyar da kungiyar Islamic State of West Africa, ISWA mai alaka da kungiyar Boko Haram ta hallaka a cikin kwana-kwanan nan.

A ranar Litinin 1 ga watan Afrilu ne ISWA ta saki faifan bidiyon yadda ta kashe sojojin Najeriya biyar a jihar Borno ta kafar yadda labarai na AMAQ.

Ahmad Salkida, dan jaridan nan da ya shahara a kan kawo rahotanni a kan ta'addanci da ake aikatawa a yankin Tafkin Chadi ne ya bayyana sunayen sojojin da aka hallaka a cikin bidiyon.

DUBA WANNAN: Ziyarar Buhari: CAN ta mayarwa NCEF martani

Jerin sunayen sojojin Najeriya da ISWA ta hallaka

Jerin sunayen sojojin Najeriya da ISWA ta hallaka
Source: Twitter

A cewarsa, galibin su dakarun sojojin Najeriya ne amma suna aike ni tare da rundunar hadin gwiwa na Civilian JTF a Doron Baga a jihar Borno.

"Mafi yawancin su mambobin Civilian JTF ne a Doron Baga. Sunayensu daga hagu: Muhammad, Na-Allah, Auwali, Grema sai na karshen kuma Sojan Ruwa ne kuma shi kadai har yanzu ba a gano sunansa ba," kamar yadda Mr Salkida ya rubuta a shafinsa na Twitter.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel