Bafarawa yace munafukai ne ke cewa an samu ci gaba a gwamnatin Buhari

Bafarawa yace munafukai ne ke cewa an samu ci gaba a gwamnatin Buhari

Tsohon gwamnan jihar Sokoto, Alhaji Attahiru Bafarawa ya yi wa gwamnatin Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari hannunka mai sanda kan abubuwan da ke faruwa a kasar.

A wata hira da yayi da shafin BBC, Bafarawa ya bayyana rashin tsaro a matsayin babbar kalubale da kasar ke fuskanta, inda ya yi nuni ga matsalar garkuwa da mutane don karbar kudin fansa a matsayin lamari da ya ki ci, ya ki cinyewa.

Ya bayyana cewa bai ga wani ci gaban da aka samu ba a kasar tun bayan da gwamnatin APC ta karbi ragamar mulki, inda ya ce gara gwamnatin baya sau dubu.

Bafarawa yace munafukai ne ke cewa an samu ci gaba a gwamnatin Buhari
Bafarawa yace munafukai ne ke cewa an samu ci gaba a gwamnatin Buhari
Asali: Depositphotos

Hakazalika tsohon gwamnan ya ce ana nuna bangaranci wajen gudanar da ayyukan ci gaba a kasar.

Ya yi kira ga shugaban kasar da ya bude kunnunwansa domin sauraren shawarwari da za su iya kawo ci gaba a kasar.

A wani lamari na daban, Legit.ng ta rahoto a baya cewa majalisar tattalin arziki ta jaridar Daily Trust, ta shawarci shugaban kasa Muhammadu Buhari akan daukan kyawawan matakai domin dawo da Najeriya bisa turba ta aminci wajen cire ta daga jerin kasashen duniya da ke sahu na gaba ta fuskar katutu na talauci.

Masana tattalin arziki na babbar jaridar sun shawarci sun shugaban kasa Buhari akan shimfida tsare-tsare cikin shekarar farko a wa'adin sa na biyu wajen tsarkake kasar nan daga kangi da kuma katutu na kuncin rayuwa mai hade da talauci.

Kungiyar zakakuran akan tattalin arziki ta shawarci shugaban kasa Buhari cikin wata sanarwa da sa hannun shugaban ta, Farfesa Ode Ojowu, da ya gabatar a ranar Litinin yayin ganawa da manema labarai a garin Abuja.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel