A karo na farko Shugaba Buhari ya yi magana akan zaben Kano

A karo na farko Shugaba Buhari ya yi magana akan zaben Kano

Dubunnan mutane da manyan kungiyoyi, sun yi ta maganganu daban-daban akan sakamakon zaben gwamnan jihar Kano, inda wasu suke kalubalantar shugaba Buhari da cewar ya yi shiru akan zarge-zargen da ake yi na amfani da 'yan daba dan ta da tarzoma a zaben da aka yi na jihar

Mai magana da yawun shugaban kasa Muhammadu Buhari, Malam Garba Shehu, ya yi wa manema labarai bayani, a wata hira da suka yi da shi kan lamarin.

Ga bayanin da Malam Garba Shehu ya yi: "Kira da ake ta yi ace wai shugaba Buhari ya binciki zaben Kano, ko shugaba Buhari ya soke ko kuma ya dauka ya bawa wani, shugaban kasa ba shi da ikon yin hakan a dokar kasa. Kuma kada a manta cewa shi kansa shugaban kasa Muhammadu Buhari kafin Allah ya bashi wannan matsayi, sau uku ya na yin takarar nan ta shugaban Najeriya ana cewa an kada shi, duk san da aka ce an kada shi zai dauki maganarsa ya kai kotu, tun daga kasa har sai ya kai kotun koli ta Najeriya."

Shugaba Buhari ya yi magana akan zaben Kano
Shugaba Buhari ya yi magana akan zaben Kano
Asali: UGC

"Mai yasa wadanda suke ganin sun fadi, ko kuma ba ayi musu adalci a zaben Kano ba, ba za su dauki maganar su je kotu kamar yadda doka ta ce ba. Idan shugaba Buhari ya ce wani abu akan wannan, ko ya kafa bincike, idan aka kawo masa sakamakon binciken mai zai yi? "

KU KARANTA: Kotu ta sa a kamo Nnamdi Kanu a duk inda ya ke

"Ba shi da ikon ya ce ya soke zabe, ba shi da ikon ya ce a dauki nasara a hannun wane a ba wa wane, kotun nan dai da aka ce aje, idan mutum ya na da shaida sai ya dauka ya je ya gabatarwa kotu shaidunsa. Ba wai ka tsaya kana zargin shugaba Muhammadu Buhari ba, mu abinda mu ke zato shi ne, so ake a narkar da matsayi da kimar shugaba Muhammadu Buhari ya ke da ita a idon al'umma, saboda bukatar gabatar da hakan ba ta yanzu ba ce.

"Gani ake yi idan ya gama mulki a 2023, duk wanda ya dauko ya ce ayi za ayi, saboda haka tunda yanzu bukata ba ta biya ba, bari nan gaba a hana shi tasiri," in ji Malam Garba Shehu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel