Boko Haram sun kai hari wani banki a jihar Adamawa

Boko Haram sun kai hari wani banki a jihar Adamawa

- Matsalar Boko Haram na ta kwan-gaba kwan-baya a Najeriya

- A yau ne 'yan ta'addar su ka kai wani hari garin Michika da ke yankin Adamawa, inda su ka fasa wani banki sannan su ka fara harbin mutane

'Yan ta'addar Boko Haram, sun kai hari wani banki a garin Michika da ke yankin jihar Adamawa, inda su ka fasa injin fito da kudi, sannan su ka fara harbin mutane.

Rahotanni sun nuna cewa, rundunar sojin bataliya ta 143 da kuma ta bataliya ta 115, sun hada rundunar hadin guiwa, su ka nufi wurin da 'yan ta'addar su ka kai harin.

Boko Haram sun kai hari wani banki a jihar Adamawa
Boko Haram sun kai hari wani banki a jihar Adamawa
Asali: Facebook

Majiyarmu LEGIT.NG ta samu rahoton cewar, rundunar sojin ta samu nasarar kashe da yawa daga cikin 'yan ta'addar, yayinda wasu daga cikinsu su ka gudu.

KU KARANTA: An kashe wata mata da diyarta a jihar Kebbi

Sojojin sun samu nasarar kwato mota mai kirar Hilux guda daya, sai masu kirar Toyota Startlet guda biyu, sannan sun kwato babura masu yawa dag wurin 'yan Boko Haram din.

Hukumar tsaro ta kasa ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta kara da cewa bayan fashin da 'yan ta'addar su ka kai sun kuma kwashi kayan abinci a yankin da abun ya shafa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel