Daga karshe, Bindow ya taya Ahmad Fintiri murna

Daga karshe, Bindow ya taya Ahmad Fintiri murna

Gwamnan jihar Adamawa, Jibrilla Bindow, ya amince da sakamakon zaben gwamnan jihar kuma ya taya. Ahmadu Umaru Fintiri, murnar nasara a zaben da aka gudanar ranar Alhamis, 28 ga watan Maris, 2019.

Bindow ya aika sako taya murnarsa ne a jawabin da ya gabatar a talabijin ga daukacin mutan jihar Adamawa.

"Dubi ga sakamako da sanarwan da INEC tayi, ina taya zababben gwamna, Ahmadu Umaru Fintiri, kan nasarar da ya samu a zaben gwamna kuma yana masa fatan alkhairi."

"A matsayina na wanda yayi imani da demokradiyya, ina girmama ka'idojin demokradiyya, kamar yadda ake yi a kasashen da suka waye."

Baturen zaben jihar Adamawa, Andrew Haruna, ya alanta Ahmadu Fintiri na jam'iyyar the Peoples Democratic Party (PDP) a matsayin wanda yayi nasara inda ya samu kuri'u 376,552 yayinda Bindow na All Progressives Congress (APC) ya samu 336,386.

Sanata AbdukAzeez Nyako na jam'iyyar African Democratic Congress (ADC) ya zo na uku da kuri'u 113,237, sannan Cif Emmauel Bello na Social Democratic Party (SDP) ya zo na hud da kuri'u 29, 792.

Baturen zaben yace: "Amadu Fintiri na PDP, bayan cika sharrudan doka kuma ya samu mafi yawan kuri'u shine zakara a wannan zabe kuma zababben gwamnan jihar Adamawa".

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel