Luwadi: Babban Fasto ya gogawa Saurayi cutar Kanjamau a jihar Legas

Luwadi: Babban Fasto ya gogawa Saurayi cutar Kanjamau a jihar Legas

Hukumar jami'an tsaron 'yan sanda ta jihar Legas, ta cafke wani babban Limamin Coci, Rabaran Ezuma Chizemdere, da aikata babban laifi na Luwadi da Samari da a halin yanzu daya daga cikin su ya kamu da cutar Kanjamau.

Luwadi: Babban Fasto ya gogawa Saurayi cutar Kanjamau a jihar Legas
Luwadi: Babban Fasto ya gogawa Saurayi cutar Kanjamau a jihar Legas
Asali: UGC

Rabaran Chizemdere wanda ya kasance babban Limamin Cocin Jesus Intervention Household Ministry da ke yankin Ejigbo na jihar Legas, ya yi kaurin suna da laifin zakkewa Samari a yankunan.

Rahotanni sun bayyana cewa, hukumar 'yan sanda ta shiga cikin wannan lamari gadan-gadan a ranar 22 ga watan Janairun 2019, inda ta samu nasarar cafke Rabaran Chizemdere kamar yadda kakakin hukumar 'yan sanda, Bala Elkana ya bayyana.

Bincike ya tabbatar da cewa, Babban Limamin ya aikata alfashar sa da kimanin Samari 15, inda ya kakabawa daya daga cikin su, Shedrack mai shekaru 16 Cutar Kanjamau kamar yadda majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito.

KARANTA KUMA: Saurayi ya kashe Budurwar sa a jihar Ondo

Yayin da za a gurfanar da shi gaban Kuliya da zarar bincike ya kammala, kakakin 'yan sandan ya ce Rabaran Chizemdere ya amsa laifin sa tare da ikirarin yadda ya ke biyan kowane Saurayi N2000 a duk sa'ilin da ya biya bukatar sa da su.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel