Yau ce ranar raba gardama a jihar Adamawa

Yau ce ranar raba gardama a jihar Adamawa

- A yau ne za a zare tsakanin jam'iyyar APC mai mulki da babbar jam'iyyar adawa PDP, a jihar Adamawa

- A zaben da aka gabatar a baya hukumar zabe ta nuna rashin gamsuwarta a zaben wasu yankuna a jihar, inda ta dakatar da zaben har zuwa wannan ranar

A yau Alhamis 28 ga watan Maris za a gabatar da zaben gwamnoni a jihar Adamawa karo na biyu. Inda aka wakilta wani mataimakin shugaban hukumar 'yan sanda na kasa akan ya sanya ido akan zaben.

Zaben wanda za a gabatar da shi tsakanin gwamnan jihar Jibrilla Bindow, wanda ke a jam'iyyar APC mai mulki, da abokin hamayyarshi Ahmadu Fintiri, da ke a babbar jam'iyyar adawa wato PDP.

Majiyarmu LEGIT.NG ta samu rahoton cewar AIG Haruna Huzi Mshellia da kuma kwamishinan 'yan sanda na jihar ta Adamawa, Adamu Audi Madaki, su ne za su sanya ido akan zaben.

Yau ce ranar raba gardama a jihar Adamawa
Yau ce ranar raba gardama a jihar Adamawa
Asali: Facebook

Kafin a dakatar da zaben, wanda aka gabatar ranar 9 ga watan Maris, Fintiri, ya na da kuri'u 367,471, sai kuma Bindow, wanda ke da kuri'u 334,995. Sakamakon zaben ya nu na cewa Fintiri ne ya ke a kan gaba da kuri'u 32,476.

Bayan haka kuma hukumar zabe ta kasa ta soke kuri'u 40,988 dalilin da ya sa hukumar ta daga zaben kenan a wasu sassa na jihar.

KU KARANTA: Akwai yiwuwar a sake sabon zaben shugaban kasa a Najeriya

A halin da ake ciki yanzu dai kowacce jam'iyya ta bukaci 'ya'yanta da su fito su yi zabe cikin kwanciyar hankali da lumana. Sai dai kuma jam'iyyar PDP, ta yi zargin cewa jam'iyyar APC mai mulki tana da kudurin dakko 'yan daba jihar Kano da Kaduna domin su ta da fitina a zaben na yau.

Sannan jam'iyyar ta kara da cewa wasu gwamnoni guda biyu daga yankin arewa maso yamma sunyi alkawarin taimakawa jam'iyyar APC domin ta murde zaben.

Sai dai kuma ita ma jam'iyyar ta APC, ta na zargin jam'iyyar PDP akan shirin da ta ke yi na tafka magudi a zaben na yau.

Wasu rahotanni sun nuna cewa a jiya gwamnan jihar ya je shi babban birnin tarayya Abuja, sannan kuma ya je jihar Legas sun gana da tsohon gwamnan jihar, Bola Ahmed Tinubu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel