Gwamna Ganduje yace Kanawa za su ga tsarin mulki na dabam a wa’adin sa na biyu

Gwamna Ganduje yace Kanawa za su ga tsarin mulki na dabam a wa’adin sa na biyu

Mai girma gwamnan jihar Kano watau Dr Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana cewa zai yi kokarin kawo wani sabon salo na mulkin jihar a wannan wa’adin na sa na karshe bayan ganin ya samu tazarce.

Abdullahi Umar Ganduje wanda ya koma kan mulki a karo na biyu yace zai cigaba da kawowa al’ummar sa na jihar Kano irin cigaban da aka gani a karon mulkin sa na farko. Gwamnan yayi wannan jawabi ne a cikin farkon makon nan.

Babban Sakataren yada labarai na gwamnan jihar Kano watau Abba Anwar, shi ne ya fitar da wannan jawabi inda gwamnan yake cewa Kanawa za su cigaba da cin moriyar gwamnatin sa ta APC kamar yadda aka fara kamo hanya.

Malam Abba Anwar yake cewa gwamnan yayi wannan bayani ne a lokacin da shugabannin kananan hukumomin jihar Kano kaf su ka ziyarce sa domin taya sa murnar lashe zaben gwamnan jihar da aka gudanar a karshen makon jiya.

KU KARANTA: Kungiya tace zaben da aka yi a Jihar Kano abin kunya ne

Gwamna Ganduje yace Kanawa za su ga tsarin mulki na dabam a wa’adin sa na biyu
Ganduje yace za a ga samfurin mulki na dabam a wannan karo
Asali: Facebook

Jagoran wannan gayya ta shugabannin kananan hukumomi, Alhaji Lamin Sani, shi ne wanda yayi jawabi a madadin sauran Takwarorin na sa 43. Lamin Sani wanda shi ne Shugaban karamar hukumar Nasarawa ya jinjinawa Gwamnan.

Alhaji Lamin Sani ya tabbatarwa Gwamnan cewa duk su na tare da shi, ganin yadda aka sake zaben sa a karo na biyu saboda irin aikin da yayi. Shugaban karamar hukumar ta Nasarawa yace Ganduje ya cika Jagora kuma abin koyi a wurin su.

A lokacin zaben jihar Kano ne ‘yan sanda su ka kama Murtala Garo da kuma shugaban hukumar ta Nasarawa, Alhaji Lamin Sani bisa zargin tarwatsa kayan aikin zabe a cikin Nasarawa a Birnin Kano.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel