Sabon rahoto: Facebook ya lalata shafuka 2,632 da suka karya dokokin kamfanin

Sabon rahoto: Facebook ya lalata shafuka 2,632 da suka karya dokokin kamfanin

- Kamfanin Facebook ya sanar da cewa ya sankame shafuka 2,632 saboda karya dokar amfani da shafin na Facebook

- Facebook ya ce sama da shafuka 500 cikin wadanda aka sankame an bude su ne daga kasar Iran, yayin da akalla 2,000 aka bude su a kasar Rasha

- Kamfanin ya ce ya na iya bakin kokarinsa na dakatar da ire iren shafukan saboda dakile amfani da kamfaninsa wajen cin mutuncin al'umma

A yayin da kamfanin sada zumunta na Facebook ya dauki mikatin tsaftace shafukansa, a ranar Talata, kamfanin ya sanar da cewa ya sankame shafuka 2,632 da suka hada da dandaluka, akawunt na mutane da shafukansu, saboda karya dokar amfani da shafin na Facebook da kuma manhajar Instagram. Wannan kuwa ya biyo bayan sankame shafukan bogi da Facebook ya fara yi a watannin baya.

Kamfanin Facebook ya ce sama da shafuka 500 cikin wadanda aka sankame an bude su ne daga kasar Iran, yayin da akalla 2,000 aka bude su a kasar Rasha.

"Masu kula da shafukan da kuma mamallakan akawunts din na daukar kansu a matsayin 'yan gari tare da kafa shafin watsa labarai, musamman ta hanyar shafukan bogi, wanda daga bisani su ke cin mutuncin 'yan siyasa ko kungiyoyinsu da kuma wasu kafofin watsa labarai," a cewar Facebook.

KARANTA WANNAN: Super Eagles ta samu kyautar zunzurutun kudi har $60,000 bayan lallasa Masar

Sabon rahoto: Facebook ya lalata shafuka 2,632 da suka karya dokokin kamfanin
Sabon rahoto: Facebook ya lalata shafuka 2,632 da suka karya dokokin kamfanin
Asali: Twitter

Da yawa daga cikin shafukan an lalata su ne saboda korafe korafen da aka tura akansu, a cewar sanarwar. Wasu daga cikin shafukan an kirkire su ne domin yada labaran da suka shafi siyasa da rikicin da ya mamaye Ukraine.

Masu bude shafukan bogi na biyan akalla $15,000 domin sayen shafin tallace tallace a Facebook, la'akari da tallar farko da kamfanin ya fara bada damar saya a watan Disambar 2013. Kamfanin Facebook ya ce akalla mutane 1.4m ne ke bin ire iren wadannan shafukan.

"Muna iya bakin kokarinmu na ganowa tare da dakatar da ayyukan ire iren wadannan shafukan saboda bama bukatar ace ana amfani da kamfaninmu wajen cin mutuncin al'umma," a cewar Facebook.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel