Wani jirgi da ya ta so daga Landan zai je Jamus ya yi batan hanya

Wani jirgi da ya ta so daga Landan zai je Jamus ya yi batan hanya

- Jirgin kamfanin British Airways ya yi batan hanya ya sauka a kasar da ba nan ya kamata ya je ba

- Da saukar jirgin a kasar ta Scotland ya kara tashi ya nufi kasar Jamus da fasinjojin jirgin, inda dama nan ne ya kamata ya je

Fasinjojin wani jirgi da ya ta so daga filin sauka da tashin jirage na birnin Landan, sun cika da mamaki, yayinda suka tsinci kan su a birnin Edinburgh, da ke kasar Scotland, saboda su dai sun san cewa a birnin Dusseldorf da ke kasar Jamus ya kamata su sauka.

Wani jirgi da ya ta so daga London zai je Germany ya yi batan hanya
Wani jirgi da ya ta so daga London zai je Germany ya yi batan hanya
Asali: Original

Hakan ya faru ne saboda matsalar da aka samu ta na'ura mai kwakwalwa, inda su ma'aikatan jirgin su ke ganin kamar suna kan hanyar zuwa birnin Dusseldorf ne, bayan abin ba haka yake ba.

KU KARANTA: Najeriya na bukatar N10trn don habaka tattalin arziki - Fashola

Bayan saukar su a birnin Edinburgh, ma'aikatan jirgin su ka baiwa fasinjojin hakuri, tare da fada musu cewar za a saka wa jirgin mai sai su wuce zuwa kasar ta Jamus, jim kadan bayan kammala sawa jirgin mai suka sa ke tashi suka nufi birnin Dusseldorf na kasar Jamus.

A karshe kamfanin jirgin sun baiwa fasinjojin hakuri tare da tabbatar musu da cewar zasu yi kwakkwaran bincike akan yanda aka yi wannan matsalar ta faru.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel