Wasu mutane daga ketare aka kawo su kayi zabe a Kano inji Kwankwaso

Wasu mutane daga ketare aka kawo su kayi zabe a Kano inji Kwankwaso

Jagoran jam’iyyar PDP a jihar Kano, Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso, ya fito yayi magana tun bayan da hukumar zabe na kasa watau INEC ta tabbatar da cewa jam’iyyar APC ce ta lashe zabe a jihar.

Wasu mutane daga ketare aka kawo su kayi zabe a Kano inji Kwankwaso
Kwankwaso yace tun da yake bai taba ganin irin magudin zaben Kano ba
Asali: UGC

Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya nuna cewa abubuwan da su ka faru a zaben cike-gibin da aka yi a jihar Kano su na cike da ban takaici da bakin-ciki. Sanatan yace ko a irin su Kasar Somaliya, ba za a ga irin abin da ya faru a zaben Kano ba.

Rabiu Kwankwaso yace duk da yana alfahari da kasar sa Najeriya, yace amma babu inda irin abin da ya faru a Kano zai faru a Duniya sai wannan kasar. Wannan jawabi ya zo mana ne ta hannun wani Hadimin Sanatan mai suna Saifullahi Hasan.

KU KARANTA: Tsohon Kwamishinan Kwankwaso yayi Allah-wadai da zaben Kano

‘Dan majalisar yake cewa jam’iyyar APC tayi hayan bakin haure ne na musamman daga irin su Nijar da su ka hargitsa kusan dukkanin inda aka karasa zaben gwamna a jihar. Kwankwaso yace wadannan mutane ne su kayi zabe ba ‘Yan Kano ba.

Injiniya Rabiu Kwankwaso yace an yi zaben ne cike da rashin adalci domin a cewar sa an fatattaki Wakilan PDP da sauran jama’a musamman mata daga rumfunan zabe. Tsohon gwamnan yace daga nan ne aka kada lissafin karya aka ce an yi zabe.

KU KARANTA: An rusa hoton Sarki Sanusi II a gidan Gwamnatin Kano bayan APC ta ci zabe

Tsohon gwamnan na Kano yake cewa wadanda su ka murde zaben, sun rika ba jam’iyyar PDP kuri’un da su ka ga dama; daga 1, 2 ko 3, inda a wani akwatin ma kaf aka rasa wanda ya zabi jam’iyyar adawar saboda tsabar magudin da aka tafka.

Kwankwaso yace idan aka cigaba da tafiya a kan rashin adalci, Najeriya za ta shiga cikin wani mugun hali maras kyau. Kwankwaso yace tsantsangoron zalunci kurum aka tafka a Kano, yana mai cewa babu mutum daya da yayi zabe a Kauyen sa.

Injiniya Kwankwaso ya kuma yabawa Kwamishinan ‘yan sandan Kano wanda a daf da zabe aka turo manyan sa da aka zarga da murde zabe. Sanatan yace ana tunanin duk ana yi wa Kano wannan ne saboda 2023 da babu wanda ya san wa zai gan ta.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel