An rage kudin sadaki a Najeriya

An rage kudin sadaki a Najeriya

- A dai-dai lokacin da samari suke ta faman korafi akan tsadar aure a Najeriya, sai ga wani malami yana bada fatawar cewa kudin sadaki shine ya zama wajibi ga miji muddin har ka'idar da addinin Musulunci ya gindaya za abi, sannan malamin ya bayyana adadin kudin sadakin da miji ya kamata ya biya

An rage kudin sadaki a Najeriya
An rage kudin sadaki a Najeriya
Asali: Original

Wani babban Malamin addinin Musulunci a kasarnan, Dr Abdulhameed Shu'aib Agaka, ya bayyana N13,438 a matsayin ainahin kudin sadakin aure a addinin musulunci.

Sannan ya kara da cewa, addini ya halatta, idan miji yana da hali ya biya fiye da yanda shari'a ta bayyana.

A lokacin da yake bayani, a gidan radiyo a garin Ilorin dake jihar Kwara, Dr. Agaka, wanda yake tsohon Malami ne a jami'ar Bayero dake Kano, yace duk wani aure da aka yi shi ba tare da an biya sadaki ba, to bai hallata ba a musulunci.

KU KARANTA: PDP zata ja daga idan ba'a baiwa Abba Kabir Gwamnan jihar Kano ba

Miji shine yake bada sadaki ga mata, domin nuna girmamawa a gareta, da kuma kara bada tabbacin cewa duk wasu lamura nata sun dawo kanshi.

Sannan ya kara da cewa a musulunce ana iya amfani da shanu, filaye, gonaki, zinare da wasu abubuwa dai masu muhimmanci wurin biyan sadaki.

A karshe Malamin ya shawarci Musulmi da su dinga bin dokar da Allah da Manzonsa suka gindaya, musamman ma ta fannin aure, domin kaucewa zinace-zinace.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng