Shugaba Buhari ya yi magana akan rashin ilimi a Najeriya
- A dai-dai lokacin da idon al'ummar kasar nan yake kan Shugaban kasa Muhammadu Buhari, domin ganin irin rawar da zai taka a wannan sabuwar gwamnatin tasa, sai gashi a karon farko Shugaban kasar yayi wata muhimmiyyar magana akan harkar ilimi a kasar nan
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce rikice-rikicen da ake fama dasu a kasar nan suna da nasaba da rashin ilimin da mutanen mu suke da.
A lokacin da yake bayani a wurin taron jami'ar National Open University of Nigeria (NOUN), wanda aka gabatar a jiya Asabar, inda ya ce gwamnatinsa zata yi kokari wurin inganta ilimi a kasar nan.
Wannan shine dalilin da yasa gwamnatin Najeriya take iya bakin kokarinta wurin ganin ta saukaka harkar ilimi a kasar nan. Saboda haka hukumar ilimi ta cire dukkanin wata katanga da zata hana wasu karatu a kasar nan.
KU KARANTA: PDP zata ja daga idan ba'a baiwa Abba Kabir Gwamnan jihar Kano ba
Sannan gwamnatinmu zata cigaba da kokari domin ganin ta kawo ababen cigaba a fannin ilimin jami'a, domin cigaban al'ummar kasar nan.
A lokacin da yake yabawa jami'ar ta NOUN, akan irin kokarin da take wurin bawa al'ummar kasar nan ingantaccen ilimi.
A bayanin da yayi shugaban jami'ar Farfesa Abdalla Adamu, yace jami'ar ta yaye dalibai 20,799, inda dalibai 103 suka fita da babban sakamako wato (First Class).
An bayyana Bala Salhu Magaji a matsayin dalibin da yafi kowa kwazo a jami'ar.
Asali: Legit.ng