Zaben Sokoto: Yadda fusatattun matasa suka raba dan sanda da bindigarsa

Zaben Sokoto: Yadda fusatattun matasa suka raba dan sanda da bindigarsa

Wasu fusattatun matasa a Sokoto sun kwace wa wani dan sanda bindigarsa bayan ya yiwa wani matashi da ya zo kada kuri'arsa rauni a kai a rumfar zaben Magajin Gari 'A' da ke karamar hukumar Sokoto na Arewa yayin zaben cike gibi na gwamna da akayi a ranar Asabar.

Dan sandan da ba a fadi sunansa ba yana kokarin daidaita al'umma ne a kan layin zabe inda ya yi amfani da sanda ya bugi yaron a kansa duk da cewa ba layin zaben ya ke ba ma.

Bayan bugun da ya yi masa, jini ya fara zuba daga kan matashin wanda hakan ya harzuka sauran matasan da ke wurin zaben inda suka rantse sai sun kashe dan sandan.

DUBA WANNAN: El-Rufai ya bayyana abinda zai yiwa wadanda ba su zabe shi ba

Zaben Sokoto: Yadda fusatattun matasa suka raba dan sanda da bindigarsa
Zaben Sokoto: Yadda fusatattun matasa suka raba dan sanda da bindigarsa
Asali: Depositphotos

A kokarin tsira da ransa, dan sandan ya yi kokari ya kubce daga hannun matasan da suka taso masa sai dai ya rasa bindigansa garin gudu.

Matasan sun karbi bindigar kuma suka rufe kofar shiga da fita daga harabar inda ake kada kuri'an hakan yasa dan sandan ya rasa inda zai bi ya tsere.

Daga bisani dai wani jami'in dan sandan ya yi ta rokon matasan tare ba su hakuri sannan suka mika masa bindigan bayan ya yi alkawarin zai biya kudin magani da za a kai matashin asibiti.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel