Kwankwaso da Mabiyan sa sun cire jajayen huluna a Jihar Kano

Kwankwaso da Mabiyan sa sun cire jajayen huluna a Jihar Kano

Mun samu labari cewa tsohon gwamnan jihar Kano watau Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso da Mabiyan sa sun cire jajayen hulunan da su ka saba sanyawa yayin da ake shirin zaben cike-gibi a Kano.

A daidai lokacin da ake shirin gudanar da karashen zaben gwamna a jihar Kano inda za a fafata tsakanin gwamna mai-ci Abdullahi Ganduje da Abba Kabir Yusuf wanda aka fi sani da Abba Gida-gida, Kwankwaso ya ajiye har hular sa.

Tun a cikin tsakiyar makon nan ne babban Jagoran na Kwankwasiyya a Najeriya, Sanata Rabiu Kwankwaso ya nemi Magoya bayan sa da su tafi hutun sa jar hular da ta zaman masu tambari a fadin jihar Kano da ma wajen cikin jihar.

KU KARANTA: ‘Dan takarar Gwamnan APC yana cikin halin wayyo ni Allah

Kwankwaso da Mabiyan sa sun cire jajayen huluna a Jihar Kano
Saifullahi Hassan ya dauki hoton Kwankwaso da hular kube
Asali: Facebook

Tsohon gwamnan ya nemi Mabiyan na sa su sanya wasu kalar huluna dabam a Ranar Asabar da za a gudanar da zabe a wasu bangarorin jihar domin su saje da sauran jama’an gari. Kwankwaso yace hakan zai ba su damar yin basaja.

Babban ‘dan siyasar yace ‘Yan Kwankwasiyya za su ajiye jar hular su ne a yau Asabar domin gudun bata-garin ‘yan adawa su shigo cikin su dauke da jar tagiya su kawo rikicin da zai jawo babban rashi a zaben gwamnan da za ayi

Wani Hadimin Sanatan na Kano ta tsakiya ya fitar da hoton Jagoran na Kwankwasiyya dauke da wata hula ta zanna-bukar mai dauke da wani launin da ba ja ba. An dai yi shekara da shekaru ba a ga Kwankwaso ba tare da jar hula ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel