Namijin kishi: Miji ya kashe kwarton matarshi

Namijin kishi: Miji ya kashe kwarton matarshi

Rundunar yan sanda a jihar Ogun ta kama wani dan shekaru 25 Ajibade Olumuyiwa da laifin kashe kwarton matarsa, Olakiitan Balogun wanda ya kasance mai sana’ar gyaran takalmi.

An kama Olamuyiwa a ranar 17 ga watan Maris, da misalin karfe 1:45am a Donald Estate Ajuwon.

An zarge shi da kashe mamacin ne a gidansa da ke Donald Estate, wanda hakan ya janyo hankulan makwabta.

Olumuyiwa ya shiga gidansa misalin karfe 12:30 na dare bayan labari da ya samu daga mai gadin gidan na cewa wani mutum yana a cikin gidansa tare da matarsa.

Namijin kishi: Miji ya kashe kwarton matarshi
Namijin kishi: Miji ya kashe kwarton matarshi
Asali: Depositphotos

An tattaro cewa mai laifin ya bar gida kimanin watanni takwas da suka gabata sannan ya kasance yana biyan mai gadin kudi don bincika mishi matarsa wacce ya saba yiwa zargin cin amana.

Amman ita matar, mai suna Titilay Olayiwola, ta musanta cewa Balogun masoyinta ne, tayi ikirarin cewa ya zo gidan ne tare da masoyiyarsa .

Ta fada wa yan sanda cewa mijinta ya hau Balogun da duka ba tare da sauraran bayanai daga gareta ko daga bakin masoyiyar Balogun ba wacce ta kasance a inda lamarin ya auku.

KU KARANTA KUMA: Ganduje ya sake kaddamar da wasu ayyuka a Gama yan kwanaki kafin zabe

Kakakin yan sanda Abimbola Oyeyemi yace DSP Ajuwon da kuma CSP Afolabi Kazeem, sun jagoranci kwararru zuwa unguwan don kama mai laifin.

Yace a halin yanzu gawar mamacin na a dakin akiye gawawwaki, inda ya kara da cewa kwamishinan yan sanda Ahmed Illiyasu ya bada umurnin tura lamarin zuwa fannin dake kula da laifi da ya shafi kisan kai don gudanar da cikakkiyar bincike da kuma gurfanar da mai laifin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel