Rayuwata na cikin hadari don Allah ku taimakeni – Inji Alaramma Ahmad Sulaiman

Rayuwata na cikin hadari don Allah ku taimakeni – Inji Alaramma Ahmad Sulaiman

Shahararren mahaddacin Al-Qur’anin nan da masu garkuwa da mutane suka yi awon gaba dashi, Ahmad Sulaiman ya yi magiya ga al’ummar Musulmai game da halin da yake ciki, inda ya bayyana cewa yana matukar bukatar taimako a halin da yake ciki.

Legit.ng ta ruwaito Alaramman ya bayyana haka ne yayin da yake magana da wani amininsa mai suna Malam Nasiru daga sansanin da masu garkuwan suke rike dashi, inda ya bayyana masa cewa su dage, su yi kamar suna yi don su cetoshi daga halin da yake ciki.

KU KARANTA: Innalillahi wa Inna Ilaihi raji’un: Mai martaba Sarkin Patigi ya rasu

“Bayanin da nake so na maka shine don Allah ka nemi shugaba, ka fada masa maganan nan ba karamar magana bace, ba maganan neman taimako a Masallatai bane, ku dubi Allah ku taimakeni, ku agajeni Malam Nasiru, ku ceci rayuwata.

“A nemi kudi, koda gidajena ne da suke Kano za’a saida a sayar, har da motar duk a hada a sayar, a hado kudin nan don Allah don zatin Allah, kum duk wanda za’a gayawa ya taimaka, shugaba ya san gwamnoni dayawa ai, kada kuyi wasa da rayuwata, ina cikin hadari sosai.

“Abinda suke fada min shine wallahi taimakona suka yi, ka kira shugaba, ka kira Malam Kabiru Gombe, ka fada ma Malam Abubakar Gero ya nemi gwamnan Kebbi ya fada masa halin da nake ciki, ka kira Malam Yakubu Musa ya fada ma gwamnan Katsina halin da nake ciki.” Inji shi.

Daga karshe Alaramman ya shaida ma abokinsa cewa shugaban masu garkuwan ya bayyana cewa idan babu wata magana zasu dauki matakin halakashi, sa’annan yace yan fashin sun bayyana bacin ransu da yadda aka ce wai ana neman taimako daga Masallaci.

A wani labarin kuma Shugaban miyagun barayin da suka yi garkuwa da fitaccen mahaddacin Al-Qur’anin nan, Alaramma Ahmad Sulaiman ya bayyana cewa wani babban dan siyasa daga jahar Kebbi ne ya biyasu donsu halaka shi, inda yace naira miliyan dari uku ya biyasu.

Shugaban barayin ya bayyana haka ne cikin wani hira da yayi da wani aminin Malamain ta wayar tarho, inda ya nemi sai an biyasu akalla naira miliyan 300, da kuma kudin man da suka kona kafin su saki Alaramma.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel