Duk wanda ya ci zaben Gwamna a Kano, a ba shi kurum a huta – Sheikh Kabara
Mun samu labari cewa babban Shehin darikar Qadriyyah na Afrika watau Sheikh Dr. Abduljabbar Nasiru Kabara, yayi kira ga gwamnatin tarayya da ta sa baki game da zaben gwamnan jihar Kano.
Abduljabbar Nasiru Kabara yayi wannan kira ne a Ranar Juma’ar da ta wuce a majasalin karatun Rayuwa bayan mutuwa da yake gabatarwa. Shehin Malamin yace hukumar INEC ta ba duk wanda ya lashe zaben da aka yi nasara.
Malamin ya kuma yi kira ga shugaban kasa Buhari da ya nemi wata dama ya ba duk wanda ya sha kasa a zaben da aka yi, bayan nan kuma ya nemi a zauna a kafa sharadi idan an gama zabe saboda gudun rikicin siyasa ya sake barkewa.
KU KARANTA: Ministan Buhari ya jinjinawa aikin sabon Kwamishinan ‘Yan Sandan Kano
Babban Malamin wanda yake gudun tsoma bakin sa a cikin lamarin siyasa yace ya zama dole yayi magana yanzu ganin yadda jihar Kano ke kokarin rincabewa. Sheikh Jabbar Kabara yace ta kai rikicin siyasa na daf da kona jihar.
Dr. Kabara yake cewa wasu baki su na shigowa cikin jihar Kano a dalilin zaben da za a karasa don haka ya jawo hankalin shugaba Buhari da cewa ya shiga cikin lamarin domin kuwa mutanen Kano sun saba ba sa goyon bayan su.
Abduljabbar Kabara ya nuna cewa matakin da hukumar INEC ta dauka na cewa ba a kammala zaben jihar ba duk wani surkulle ne domin kuwa a cewar sa alkaluma sun riga sun nuna wanda ya ci zabe don haka yace a ba sa mulki.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa
Ko a http://twitter.com/legitnghausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT
Asali: Legit.ng