Dalilin da ya sa zaben da za a maimaita a Bauchi ke firgita PDP - APC

Dalilin da ya sa zaben da za a maimaita a Bauchi ke firgita PDP - APC

Mataimakin sakataren yada labaran jam'iyyar APC na kasa, Yekeen Nabena, ya ce jam'iyyar hamayyaa, PDP, na tsoron dibar kashin ta a hannu a zaben da za a karasa a wasu mazabun jihar Bauchi a ran Asabar, 23 ga watan Maris.

A yayin hutun karshen mako ne hukumar zabe ta kasa (INEC) ta bayyana cewar ba zata kara maimaita zabe a jihar ta Bauchi ba.

Sabanin maimaita zabe, INEC ta bayyana cewar za ta cigaba da tattara sakamakon zabe a karamar hukumar Tafawa Balewa daga yau, Litinin, biyo bayan gano kwafin sakamakon zaben da wasu 'yan dabar siyasa suka yaga.

Da ya ke magana da manema labarai a yau, Litinin, a Abuja, Nabena ya ce PDP ta gamsu da mi'ara koma baya da INEC ta yi a kan batun zaben gwamnan jihar saboda sun san cewar ba zasu taba kai wa ga nasara ba idan aka maimaita sahihin zabe na gaskiya.

Dalilin da ya sa zaben da za a maimaita a Bauchi ke firgita PDP - APC
Cibiyar tattara sakamakon zabe a Bauchi
Asali: UGC

Da ya ke kare kalaman sa, Nabena ya kafa hujja da cewar jam'iyyar APC ce ta lashe mafi yawan kujerun majalisar dokokin jihar Bauchi a zaben da aka gudanar ranar Asabar, 9 ga watan Maris.

"Jam'iyyar adawa ta san cewar matukar aka maimaita zabe na gaskiya APC ce zata yi nasara.

"Ba wai nasara ce a bar dubawa ba koda yaushe a zabe, sahihancin zabe na da matukar muhimmanci, kuma mu hakan shine abinda mu ke nema; a gudanar da zabe na gaskiya koda kuwa jam'iyyar adawa zata yi nasara," a cewar Nabena.

DUBA WANNAN: Ganduje: Dakta Baffa Bichi na APC ya ziyarci Abba Gida-gida har gida

Sannan ya cigaba da cewa, "ina fadin haka ne saboda na san cewa da ba a gudanar da zabe na gaskiya ba da ba za a kai ga maganar maimaita zabe ba. Muna kira ga INEC da kar ta bawa PDP damar lashe zabe a garabasa."

A yau, Litinin, da rana ne gwamnan jihar Bauchi, Mohammed Abubakar, ya gana da shugaban kasa Muhammadu Buhari tare da shaida ma sa niyyar sa ta garzaya wa kotu domin kalubalantar matakin da INEC ta dauka dangane da zaben jihar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel