Mawaki Naziru ya roki Buhari ka da ya bari a murde zaben Kano

Mawaki Naziru ya roki Buhari ka da ya bari a murde zaben Kano

Dazu nan ne mu ka samu labari cewa babban Mawakin nan na kasar Hausa, Nazir Ahmad wanda aka fi sani da Sarkin Waka, yayi wata sabuwar waka bayan an dakatar da zaben gwamna a jihar Kano.

A wannan sabuwar waka fil da Alhaji Naziru M. Ahmad ya fitar a tsakiyar makon, ya roki Ubangiji Allah da sunayen sa tsarkaka da cewa ka da a samu wasu miyagun ‘yan siyasa da za su zo su canza sakamakon zaben jihar Kano.

Babban Mawakin ya nuna cewa wasu ‘Yan siyasa sun taso jihar Kano a gaba inda su ka rantse sai inda karfi ya kare masu wajen ganin jam’iyyar APC mai mulki ta samu nasara a zaben gwamna na jihar wanda yanzu aka daga zuwa gaba.

Wannan Mawaki mai basira ya kira sunan shugaban kasa Muhammadu Buhari wanda ya kira da Uban mutanen Kano, inda ya fada masa cewa ana neman ayi amfani da karfin iko wajen tauyewa mutanen jihar na sa zabin su na gwamna.

KU KARANTA: Kai Uba ne, ka zare kan ka daga zabukan Jihohin da za ayi – PDP ga Buhari

Mawaki Naziru ya roki Buhari ka da ya bari a murde zaben Kano
Naziru yana gudun ayi rikici idan aka murde zaben Kano
Asali: UGC

A wannan sabuwar waka da aka rangada kwanan nan, Naziru Sarkin Waka, ya fadawa shugaban kasar cewa mutanen da su ka zabe sa, su ne su ka zabi Abba Kabiru Yusuf a matsayin ‘dan takarar gwamna a zaben gwamna da aka yi.

Haka kuma Mawakin ya nemi shugaba Buhari yayi watsi da kiran da wasu ‘Yan APC su ke yi masa na ganin an yi abin da bai dace ba a zaben Kano. Mawakin yake cewa masu wannan kira, Makiyan jihar ne kuma marasa kishi.

Naziru Ahmad ya kuma tunawa shugaban kasar cewa shi ne ya fadawa jama’a su zabi duk wanda su ke so, don haka mutanen Kano su ka ki zaben gwamna Abdullahi Ganduje na APC, amma yanzu ake neman a murde zaben da aka yi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel