APC 13, PDP 9: Jerin sunayen sabbin gwamnoni da INEC ta sanar sun lashe zabe

APC 13, PDP 9: Jerin sunayen sabbin gwamnoni da INEC ta sanar sun lashe zabe

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta na Kasa INEC ta sanar da sunayen 'yan takarar gwamna 22 a cikin jihohi 29 da aka gudanar da zabe a ranar 9 ga watan Maris.

Jam'iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki tana da jihohi 13 yayin da babban jam'iyyar adawa ta Peoples Democratic Party (PDP) tana da jihohi tara.

Hukumar ta INEC ta sanar da cewa zabe bai kammala ba a jihohi biyar yayin da sakamakon wasu jihohi biyu da suka rage ba su kammala ba a lokacin da ake rubuta wannan rahoton.

Cikaken jerin sunayen gwamnoni 22 da INEC ta sanar - APC 13, PDP 9
Cikaken jerin sunayen gwamnoni 22 da INEC ta sanar - APC 13, PDP 9
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Kiri da muzu: An ga wakilan PDP na rabawa masu zabe kudi a Abuja

Jihohin da ba a gudanar da zabukkan gwamnoni ba a wannan karon sune Edo, Kogi, Ondo, Ekiti, Anambra, Osun da Bayelsa.

Ga dai jerin sunayen 'yan takarar da jihohinsu da jam'iyyun su kamar yadda INEC ta fitar:

JIHOHI ZABABUN GWAMNONI JAM'IYYUN SIYASA

1 ABIA - OKEZIE IKPEAZU - PDP

2 AKWA IBOM - UDOM EMMANUEL - PDP

3 BORNO - BABAGANA ZULUM - APC

4 CROSS RIVER - BEN AYADE - PDP

5 DELTA - IFEANYI OKOWA - PDP

6 EBONYI - DAVID UMAHI - PDP

7 ENUGU - IFEANYI UGWANYI - PDP

8 GOMBE - INUWA YAHAYA - APC

9 IMO - EMEKA IHEDIOHA - PDP

10 JIGAWA - ABUBAKAR BADARU - APC

11 KADUNA - NASIR EL-RUFAI - APC

12 KATSINA - AMINU MASARI - APC

13 KEBBI - ABUBAKAR BAGUDU - APC

14 ZAMFARA - MUKTAR IDRIS - APC

15 YOBE - MAI MALA BUNI - APC

16 NASARAWA - ABDULLAHI SULE - APC

17 NIGER - ABUBAKAR BELLO - APC

18 OGUN - DAPO ABIODUN - APC

19 OYO - SEYI MAKINDE - PDP

20 TARABA - DARIUS ISHAKU - PDP

21 LAGOS - BABAJIDE SANWO-OLU - APC

22 KWARA - ABDULRAHMAN ABDULRAZAQ - APC

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164