Zaben gwamnan Kaduna: El-Rufai ya kammala kwantar da jam’iyyar PDP
Zuwa yanzu an kammala tattara alkalumman sakamakon zaben gwamnan jahar Kaduna da aka kwashe tsawon kwanaki biyu ana tattarawa da kuma kidayarsu domin tabbatar da sahihin sakamako ba tare da zargin ka ci baka ci ba, baka ci ba ka ci.
Idan za’a tuna a ranar Asabar din data gabata, 9 ga watan Maris ne aka gudanar da zaben gwamnoni a jahohi akalla guda 30 na Najeriya, inda wasu gwamnonin dake kan kujera ne ke kokarin zarcewa, yayin da aka samu sabbin gwamnoni a wasu jahohin.
KU KARANTA: Zaben gwamna: APC ta lashe jahohi 10, PDP ta samu nasara a jahohi 5
Jahar Kaduna na daya daga cikin jihohin da gwamnanta, Nasir El-Rufai ya nemi zarcewa don yin dare dare akan karagar mulki, yayin da dan takarar jam’iyyar PDP, Isah Ashiru Kudan ya kalubalanceshi a takarar.
Amma daga karshe bayan tattara alkalumman sakamakon zaben daga kananan hukumomin jahar guda 23 gaba daya, gwamnan jahar Kaduna Nasir El-Rufai ne ya samu gagarumar nasara da bambamcin kuri’u 231, 173 inda yayi ma Isah Ashiru da jam’iyyar PDP murus kamar yadda yake cewa.
El-Rufai ya samu kuri’a 1,045,417, yayin da Isah Ashiru ya samu 814,244, Ga dai yadda sakamakon zaben ya kasance a kananan hukumomi 23 na jahar Kaduna, kamar yadda Legit.ng ta ruwaito.
1, Kubau
APC – 57,182
PDP – 17,074
2, Ikara
APC – 41,969
PDP – 22,553
3, Kudan
APC – 28,624
PDP – 22,022
4, Kaura
APC – 8,342
PDP – 38,764.
5, Makarfi
APC – 34,956
PDP – 22,301
6, Jaba
APC: 6,298.
PDP: 22,976
7, Kajuru
APC – 10,229
PDP – 34,658
8, Giwa
APC – 51,455
PDP – 19,834
9, Kauru
APC -34,844
PDP – 31,928
10, Kachia
APC – 30,812
PDP – 51,780
11, Soba
APC – 55,046
PDP – 25,440
12, Zangon Kataf
APC – 13,448
PDP – 87,546
13, Sanga
APC – 20,806
PDP – 21,226
14, Kaduna ta Arewa
APC – 97,243
PDP – 27,665
15, Birnin Gwari
APC – 32,292
PDP – 16,901
16, Chikun
APC – 24,266
PDP – 86,261
17, Sabon Gari
APC – 57,655
PDP – 25,518
18, Lere
APC – 71,056
PDP – 45,215
19, Jema’a
APC – 21,265
PDP – 63,129
20, Kagarko
APC – 21,982
PDP – 26,129
21- Zaria
APC : 111,014
PDP: 35,356
22- Igabi
APC: 102,612
PDP: 31,429
23- Kaduna ta kudu
APC: 102,035
PDP: 37,948
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng