Akwai sake a zaben gwamnonin Adamawa, Sokoto, Bauchi da Filato – Inji INEC

Akwai sake a zaben gwamnonin Adamawa, Sokoto, Bauchi da Filato – Inji INEC

A yayin da ake karkare sanar da sakamakon gwamnonin daya gudana a yawancin jahohin dake fadin Najeriya, za’a iya cewa tsuguni bata kare a wasu jahohin ba sakamakon hukumar zabe mai zaman kanta, INEC ta sanar da wasu zabukan cewa basu kammala ba.

Legit.ng ta ruwaito daga cikin jihohin da aka samu irin wannan tasgaro akwai jahar Bauchi, Sakkwato, Adamawa da kuma jahar Filato, dukkaninsu jihohi ne dake Arewacin Najeriya

KU KARANTA: Karen batta: Kalli jerin manyan lauyoyi 18 da zasu kare Buhari a shari’arsa da Atiku

Sai dai babban dalilin da doka ta tanadar na auna idan zabe bai kammala ba shine idan har bambamcn kuri’un dake tsakanin jam’iyyun dake kan gaba ya kasance bai whaura adadin kuri’un da suka lalace ko kuma wadanda INEC ta soke ba.

Ma’ana idan har adadin lalatattun kuri’u yah aura adadin kuri’un dake tsakanin na daya da na biyu, tabbas wannan zabe bai kammala, anan sai hukumar INEC ta yi nazari don gano inda aka samu matsalar tare da shirya sabon zaben maimaici a irin wadannan wurare don samun karin kuri’u da zasu tabbatar da sahihin wanda ya lashe zabe.

An samu irin haka a jahar Adamawa, babban baturen zabe na jahar, Farfesa Andrew Haruna ya sanar da rashin kammaluwar zaben sakamakon kashe zaben da aka yi a rumfuna 44 a fadin jahar, da kuma rashin gudanar da zabe a wasu rumfunan.

Haka zalika a jahar Sakkwato, inda gwamna Aminu Tambuwal na PDP ke kan gaba da kuri’u 489,558, yayin da dan takarar APC Ahmed Aliyu keda 486,145, bambamcin kuri’u 3,413, amma akwai kuri’u sama da 75,000 lalatattu da kuma wadanda aka soke.

Hakan take a jahar Bauchi, inda baturen zabe Farfesa Mohammed Kyari yace zaben bai kammala ba saboda soke sakamakon zaben karamar hukumar Tafawa Balewa sakamakon rikici daya balle a garin, zaben da yace zasu maimaita cikin kwanaki 21, duk da dai PDP ke kan gaba da kuri’u 469,512, yayin da APC keda 465,453.

Bata sauya zani a jahar Filato ba, inda APC ke kan gaba da kuri’u 583, 255, yayin da PDP keda 538,326, sai dai baturen zaben, Richard Kimbir yace zasu gudanar da zaben maimaici a kananan hukumomi 14 cikin 17 na jahar.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel