Gwamna Masari ya doke PDP ya ci zaben Katsina a karo na biyu
- Mai Girma Aminu Masari ya lashe zaben 2019 na Gwamnan Jihar Katsina
- Gwamnan ya samu zarcewa a kan mulki bayan ya doke Lado Y. Danmarke
- Masari ya samu kuri’a 1,178,864 yayin da PDP kuma ta iya samun 488,621
Hukumar zabe na kasa watau INEC ta tabbatar da cewa gwamna Aminu Masari ya lashe zaben 2019 na Gwamnan Jihar Katsina da aka yi a karshen makon nan. Masari ya samu tazarce ne a karkashin jam’iyyar APC mai mulki.
Farfesa Abdu Zuru na jami’ar Usmanu Danfodio da k e Sokoto ya sanar da sakamakon zaben inda ya bayyana cewa Jam’iyyar APC ta samu kuri’u 1,178,864 inda Sanata Yakubu Danmarke PDP ya zo na biyu ta samu kuri’a 488,621.
‘Yan takara kusan 18 ne su kayi takarar kuma da alamun cewa jam’iyyar PDP ba ta amince da sakamakon zaben ba. Gwamna Masari dai ya lashe zaben da aka yi a cikin duka kananan hukumomin da ake da su a fadin jihar.
KU KARANTA: Gwamna El-Rufai yana kan gaba a zaben Gwamnan Jihar Kaduna
Ga kadan daga sakamakon kananan hukumomin na Katsina:
Danmusa
APC- 28,008
PDP- 10,306
Batagarawa
APC- 39,420
PDP- 12,512
Kankia
APC- 29, 096
PDP- 14,706
Maiadua
APC- 34,154
PDP- 12,904
Batsari
APC- 33,742
PDP- 14,142
KU KARANTA: INEC ta dakatar da zaben Gwamna a wani Kauyen Zamfara
Ingaawa
APC 28,905
PDP 12,602
Baure
APC 41,076
PDP 18,012
Rimi
APC 36278
PDP 12,496
Mani
APC 34,254
PDP 16,476
Katsina
APC 64,709
PDP 16,734
Karamar hukumar Dutsi
Gwamna
APC 22,482
PDP 10,564
KU KARANTA: Yadda sakamakon zaben Jihar Kaduna yake kasancewa a halin yanzu
Karamar hukumar Matazu
Gwamna APC: 28, 253
PDP: 10, 327
Karamar hukumar Kusada
Gwamna
APC 20,799
PDP 8,080
Karamar hukumar Sandamu
Gwamna
APC 32,193
PDP 11,912
Karamar hukumar Zango
APC 23, 43
PDP 11,662
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa
Ko a http://twitter.com/legitnghausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT
Asali: Legit.ng