Hanyoyi 10 da 'yan siyasa ke amfani da su wurin tafka magudin zabe a Najeriya

Hanyoyi 10 da 'yan siyasa ke amfani da su wurin tafka magudin zabe a Najeriya

A watan Fabrairu ne aka gudanar da zaben shugaban kasa da na 'yan majalisu a Najeriya kuma bayan bayyana sakamakon zaben, an rika samun zargin aikata magudin zabe da jam'iyoyin siyasa da dama.

Wannan zargin galibi ya fi zuwa ne daga jam'iyyun da suka sha kaye a zabe.

Misali a nan shine babban jam'iyyar adawa ta PDP da ke zargin cewa jam'iyyar APC mai mulki ta tafka magudi a zaben tun kafin Hukumar zabe INEC ta sanar da sakamakon zabe.

A halin yanzu dai jam'iyyun da ba su gamsu da sakamakon zaben ba sun garzaya kotu.

Premium Times tayi nazarin wasu hanyoyi da 'yan siyasa suke amfani da su wurin aikata magudin zabe a Najeriya.

Hanyoyi 10 da 'yan siyasa ke amfani da su wurin tafka magudin zabe a Najeriya
Hanyoyi 10 da 'yan siyasa ke amfani da su wurin tafka magudin zabe a Najeriya
Asali: Facebook

DUBA WANNAN: Tsaro: An fitar da kididdigar adadin mutanen da aka kashe a Zamfara cikin mako guda

1. Antaya sojoji a garuruwan da abokan hammaya

Tabbatar da cewa sojoji dauke da bindigu da sauran jami'an tsaro sun cika rumfunan zaben da abokan hammaya ke da galaba zai sanya masu jefa kuri'a su ji tsoron fitowa zabe tare da jefa fargaba a zuciyarsu.

Misali shine zaben da aka gudanar a wasu sassan Najeriya an samu barkewar rikici tsakanin 'yan bangan siyasa da sojoji inda aka kashe mutane 9 ciki har da soja guda. I

rin wannan rikicin yana janyo wa a soke zaben yankin wanda hakan na nufin abokin hammayar ya rasa kuri'un da ya kamata ya samu.

2. Tabbatar da jinkirin kawo kayan zabe a rumfar zaben abokan hammaya

Rashin kai kayan zabe a kan lokaci yana nufin ba za a fara zaben da wuri ba kuma lokacin dakatar da kada kuri'a zai iya yi ba tare da mutane sun gama zabe ba wanda hakan zai sanya abokan hammyar su rasa kuri'u.

3. Yiwa ma'aikatan INEC barazana

Galibi 'yan siyasar da ke rike da mulki suka fi amfani da wannan inda za su tilastawa baturen zabe fadin sakamakon da ba shine ainihi ba.

Misali a nan shine zaben sanata na Imo ta Yamma da aka gudanar inda aka ruwaito cewa Gwamna Rochas Okorocha ya yi kutse ofishin tattara kuri'u da ke Orlu inda daga bisani aka sanar cewa Rochas ya lashe zabe.

Sai dai kuma daga baya, baturen zabe na jihar, Mr Ibeabuchi ya ce an tilasta shi fadin sakamakon zaben na.

4. Kawo cikas ga tsarin sufuri na INEC

Hukumar zabe INEC ta dogara ne ga kungiyar direbobi na kasa NURTW wurin jigilar kayayakin zabe zuwa wuraren da za ayi zaben, hakan na nufin 'yan siyasa na iya hada baki da direbobin domin suyi jinkirin kai kayan aikin da gangan ko su lalata na'urar tantance zabe da sauransu wanda hakan zai kawo cikas ga zaben.

5. Bawa ma'aikatan INEC cin hanci

Wannan yana daga cikin tsohon dabarar da 'yan siyasa ke amfani da shi wurin magudin zabe, 'yan siyasa na iya bawa ma'aikatan INEC, ko ma'aikatan wucin gadi ko 'yan yiwa kasa hidima kudi ko kuma suyi musu alkawarin ba su aiki ko kwangila bayan sun lashe zabe.

Misali shine yadda tsohuwar ministan man fetur Diezani Alison -Madueke ta bawa ma'aikacin INEC Miliyan 30 domin ya taya su magudin zabe gabananin zaben 2015 amma duk da haka ba suyi nasara ba, an samu irin wannan abin a zaben 2019 a jihohi kamar Rivers.

Sauran hanyoyin da 'yan siyasa ke amfani da su wurin magudin zaben sun hada da

6. Sace akwatin zabe a rumfunan da abokan hammaya ke da galaba

7. Bangar siyasa da tayar da hankulan al'umma

8. Sauya alkalluman zabe a ofishin kidayar kuri'u

9. Sayan kuri'a yayin zabe

10. Tilastawa baturen zabe fadin sunanka a matsayin wanda ya lashe zabe domin abokin hammaya ya tafi kotu

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel