Hadari: Babban mota dauke da duwatsu ta markade mutane uku har lahira a Abeokuta

Hadari: Babban mota dauke da duwatsu ta markade mutane uku har lahira a Abeokuta

Mutane uku sun mutu yayin da wata babban mota dauke da duwatsu tayi hatsari a kusa da kauyen Talabi da ke kusa da babban titin Abeokuta zuwa Sagamu a yammacin ranar Laraba.

Kakakin hukumar kiyaye haddura na jihar (TRACE), Mr Babatunde Akinbiyi ne ya tabbatarwa kamfanin dillancin labarai na kasa NAN afkuwar hatsarin a ranar Alhamis a Abeokuta.

Akinbiyi ya yi bayanin cewa wata mota kirar Honda mai lamba NPK 186 da Toyota Corolla mai lamba FST 04 ER da kuma babban mota mai lamba KJA 931 XH suka yi hatsarin.

Hatsari: Babban mota ta markade mutane uku a Abeokuta
Hatsari: Babban mota ta markade mutane uku a Abeokuta
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Al'ajabi: 'Yan Najeriya 5 da ke ikirarin sun mutu, sun shiga aljannan sun dawo

"Tayar Hondan da ke kan hanyarta na zuwa Shagamu ne ya fashe hakan yasa motar ta kwacewa direban ya koma dayan bangaren titin ya yi karo da Toyota da ke hanyarta na shiga Abeokuta.

"Hakan yasa direban babban motar da ke bayan Toyotan ya yi kokarin kaucewa sauran motocci ya fada daji inda ya markade wasu mutane uku da ke tsaye a gefen titin kuma suka mutu a nan take.

"Mutane shida ne hatsarin ya ritsa da su, maza uku da mata uku. Mutane uku sun rasu yayin da sauran ukun sun jikkata," inji shi.

Akinbiyi ya ce an kai motoccin da su kayi hatsarin zuwa ofishin 'yan sanda da ke Ibara yayin da shi kuma dirban babban motar yana tsare.

Ya ce an garzaya da wadanda suka jikkata zuwa cibiyar lafiya na tarayya yayin da gawarwakin wadanda suka rasu suna babban asibitin Ijaye da ke Abeokuta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel