Tarihi: Kyawawan hotunan shugabannin Najeriya 5 da matan su

Tarihi: Kyawawan hotunan shugabannin Najeriya 5 da matan su

Najeriya tayi shugabani da dama kuma a yayin da suke jagorancin kasar akwai jaruman matansu da suka kayi gwagwarmaya tare da su kama daga kamfen, gwagwar,ayar siyasa da ruguntsumin mulkin kasar.

Matan shugabanin kasan sun taka rawa a matsayinsu na 'First Ladies' ko iyayen kasa.

A ranar Asabar 23 da ta gabata, 'yan Najeriya sun zabi Shugaba Muhammadu Buhari a matsayin wanda zai jagorance su har zuwa shekarar 2023.

Domin karrama iyalan wadanda su kayi jagorancin Najeriya, Legit.ng ta tattaro muku kayatattun hotunan shugabanin Najeriya tare da matansu tun kafin su dare kan kujerar mulki.

1) Janar Sani Abacha da Maryam Abacha

Janar Sani Abacha jami'in sojan Najeriya ne wanda daga baya ya zama shugaban kasa daga shekarar 1993 zuwa 1998. Shine soja na farko da ya taba kaiwa mukamin Janar ba tare da tsallake wata mukami ba. Ya auri matarsa mai suna Maryam Abacha.

DUBA WANNAN: APC ta soke ziyarar da Buhari zai kai zuwa wasu jihohin PDP 5

2) Olusegun Obasanjo

Olusegun Obasanjo shima tsohon sojan Najeriya ne da ya mulki Najeriya daga 1999 zuwa 2007. Obsanjo ya yi mulkin Najeriya sau biyu, ya yi mulki a matsayin soja sannan ya yi mulkin farar hula. Ya auri matarsa Stella Obasanjo wace da riga tallafa masa a lokacin mulkinsa.

3) Mariyagi Umaru Musa Yar'adua da Turai Yar'adu

Marigayi Umaru Musa Yar'adua shine shugaban kasa na 13 a Najeriya. Kafin zama shugaban kasa, ya yi gwamna a jihar Katsina daga Mayun 1999 zuwa Mayun 2007 da ya rasu. Ya rasu ne a ranar 5 ga watan Mayun 2010. Matarsa Turai 'Yar'adua ta tallafa masa yayin da ya mulki kasar.

4) Goodluck da Patience Jonathan

Goodluck Ebele Jonathan ya mulki Najeriya daga 2010 zuwa 2015. Ya kuma kasance mataimakin shugaban kasa daga 2007 zuwa 2010 yayin da Yar'adua ke mulki. Mai dakinsa Patience Jonathan ta taka muhimmiyar rawa a cikin mulkinsa.

5. Shugaba Muhammadu Buhari da Aisha Buhari

Shugaba Muhammadu Buhari shine shugaban kasa mai ci a yanzu. Ya zama shugaban kasa a 2015 kuma zai kasance a kan mulki har zuwa 2023 bayan lashe zaben 2019 da aka gudanar.

Buhari shima tsohon soja ne mai murabus. Ya mulki kasar karkashin mulkin soja daga ranar 31 ga watan Disamban 1983 zuwa ranar 27 na Augustan 1985 bayan ya yi juyin mulki. Yana auren Aisha wadda itama tana matukar bashi goyon baya a matsayinsa na shugaban kasa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel