Dalilin da ya sa mutanen Sokoto ba za su sake zabar Tambuwal ba – Zababben dan majalisa na APC

Dalilin da ya sa mutanen Sokoto ba za su sake zabar Tambuwal ba – Zababben dan majalisa na APC

Wani zababben dan majalisan wakilai a yankin mazabar Shagari-Yabo, Abubakar Umar, a ranar Lahadi, 3 ga watan Maris yace mutanen Sokoto ba za su sake zabar Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ba saboda babu aikin da yayi ma jihar.

A cewar shi, gwamnan bai gudanar da ayyukan komai ba kuma yanzu ne lokacin da mutanen jihar za su yi masa ramuwar gaiya.

Yayinda Umar ke magana da manema labarai, ya bayyana cewa “a lokacin da Bafarawa yayi gwamnan Sokoto, ya gina gidaje 500 tare da gadar sama, sannan gwamnan da ya gabata ya gina gidaje 2,000, gada da manyan cibiyoyi a fadin jihar."

Dalilin da ya sa mutanen Sokoto ba za su sake zabar Tambuwal ba – zababben dan majalisa na APC
Dalilin da ya sa mutanen Sokoto ba za su sake zabar Tambuwal ba – zababben dan majalisa na APC
Asali: Depositphotos

Ya bayyana cewa zaben shugaban kasa da na majalisa da aka gudanar kwanan nan a jihar ya kasance gwaji dake tabbatar da cewa gaba daya al’umman jihar sun gaji da lalatacciyar gwamnatin jam’iyyar PDP a jihar, haka zalika wannan ne sanadiyar su na zabar APC.

Har ila yau, ya sha alwashin cewa zai kawo musu ayyuka da dama mazabar tare da inganta shirinsa na sukolashif wanda a halin yanzu dalibai fiye da 200 sun ci amfaninsa.

KU KARANTA KUMA: Sanata Dariye na fama da matsalar gazawar koda a gidan yari

Yayinda yake mayar da martani, kakakin jam’iyyar PDP a jihar, Abdullahi Hausawa yace suna kyautata zatton lashe zaben gwamna da za a gudanar a ranar Asabar mai zuwa.

Ya ce Gwamna Tambuwal ya samu nasarori a fannin ilimi, noma, kiwon lafiya da tsaro wanda hakan zai bashi damar sake lashe zabe a karo na biyu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel