Uwa ba wasa ba: Matashin da yayi ma uwarsa yankan rago ya gamu da mummunar hukunci

Uwa ba wasa ba: Matashin da yayi ma uwarsa yankan rago ya gamu da mummunar hukunci

Wata babbar kotu dake zamanta a garin Jos na jahar Filato ta yanke hukuncin kisa ta hanyar rataya akan wani matashi mai shekaru 20, Agugu Adau, sakamakon kamashi da laifin kashe mahaifiyarsa ta hanyar yi mata yankan rago.

Legit.ng ta ruwaito Alkalin kotun, mai sharia Nafisa Musa ce ta yanke masa wannan hukunci a zaman karshe na sauraron karar a ranar Alhamis, 28 ga watan Feburairu, inda tace kwararan hujjoji sun bayyana dake nuna Adau ne ya kashe uwarsa.

KU KARANTA: Hajiya mai waina ta rabar da wainarta duka albarkacin nasarar Buhari

Uwa ba wasa ba: Matashin da yayi ma uwarsa yankan rago da gamu da mummunar hukunci
Agugu
Asali: UGC

“Duba da kwararan hujjojin da lauya mai kara ya bayyana ma kotu, babu wani tantama kai Adau kai ne ka kashe mahaifiyarka saboda tsabar rashin Imani, don haka kotu ta yanke hukuncin ratayeka har sai ka mutu, Allah yayi maka rahama.” Inji ta.

A ranar 30 ga watan Disambar shekarar 2016 ne Adau ya aikata wannan aika aika akan uwarsa wai don ta hanashi wani layar zana da yace mahaifinsa ya bar masa gado, a gonarsu dake kauyen Kisaghyip, cikin karamar hukumar Bassa ta jahar Filato.

Daga nan kuma sai ya kwashe yan kudin dake jikinta da suka kai N20,000, wanda yayi amfani dasu wajen sayan wayar salula, riga da kuma talkalmi. Da aka zanta da Adau ga binda yace: “Tun ina dan shekara 14 marigayi mahaifina wanda tsohon boka ya nuna min wata laya dake sa mutum ya bace kuma ya dawo.

“Kuma yayi alkawarin bani wannan laya idan har na kai shekara 18, shekaru hudu da suka wuce a lokacin da yake gadon ajali sai ya baiwa mahaifiyata layar, yace mata ta bani idan na kai shekaru 18, a yanzu na kai 18, amma ta hanani.

“A ranar na sameta a gona, inda na nemi ta bani layar, sai taki, har ma tayi barazanar jefa shi a cikin ruwa idan na dameta, daga nan na fahimci bata da amfani a wajena a matsayinta ta uwa, nan take na kwantar da ita na yankata da wukar da muke girban dankali. Na kuma jefa gawarta a daji.” Inji shi.

Sai dai yayansa, David ya karyata batun layar zana cikin kisan mahaifiyarsu da Agugu yayi, inda yace ya kasheta ne kawai don ya kwashe N20,000 da shi ya bata ajiye, saboda a lokacin yana aiki a barikin ladi, kuma babarsu ke ajiye masa yan kudadensa.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel