Dalilin da ya sanya Ganduje, Masari, Gaidam suka gaza cika alkawurran su na zaben Buhari

Dalilin da ya sanya Ganduje, Masari, Gaidam suka gaza cika alkawurran su na zaben Buhari

Da yawa daga cikin mashahuran 'yan siyasa da kungiyoyi masu ruwa da tsaki akan harkokin siyasa, sun gaza cika alkawurran su na tanadar tumunin kuri'u ga shugaban kasa Muhammadu Buhari yayin babban zaben kasa da aka gudanar a makon da ya gabata.

Makonni kadan gabanin babban zaben kasa da aka gudanar a ranar Asabar, 23 ga watan Fabrairun 2019, gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje, ya yiwa shugaban kasa Buhari alkawarin kuri'u kimanin miliyan biyar na al'ummar jihar Kano.

Kamar yadda shafin jaridar Daily Trust ya ruwaito, gwamna Ganduje ya gaza cika wannan alkawari yayin da shugaban kasa Buhari ya samu kuri'u miliyan 1.4 kacal na al'ummar jihar Kano a zaben da aka gudanar.

Gwamna Ganduje tare da shugaban kasa Buhari a fadar Villa
Gwamna Ganduje tare da shugaban kasa Buhari a fadar Villa
Asali: UGC

Wani dalibin jami'ar Bayero dake jiar Kano, Abdullahi Yunusa, yayin bayyana ra'ayin sa ga manema labarai dangane da harkokin siyasa a kasar nan, ya ce 'yan siyasa da dama su kan yi ƙari a zantukan su domin kawai su burge magoya baya.

Gwamna Ganduje yayin amsa tambayoyin manema labarai a fadar shugaban kasa da ke babban birnin tarayya Abuja, ba ya ga taya murna ta nasarar shugaban kasa Buhari ya ce al'ummar jihar Kano sun gaza tanadar kuri'u miliyan biyar sakamakon rashin fitowar su wajen kada kuri'u yayin zabe.

Baya ga jihar Kano, gwamna Aminu Bello Masari na jihar Katsina, ya gaza samar da kuri'u miliyan 2.8 sabanin yadda ya sha alwashi, inda shugaba Buhari ya samu kuri'u miliyan 1.2 kacal a yayin babban zabe.

KARANTA KUMA: Kungiyar Matasan Ibo ta bayyana dalilin da ya sanya ta yi goyon bayan Buhari a zaben 2019

Kazalika gwamnan jihar Yobe, Ibrahim Gaidam, ya gaza cika alkawarin sa na samar da kaso 98 cikin 100 na adadin kuri'un al'ummar jihar sa ga shugaban kasa Buhari, inda ya samu kaso 88.4 yayin babban zaben kasa na makon da ya gabata.

Jaridar Legit.ng kamar yadda gwamnonin su ka zayyana ta fahimci cewa, dukkanin su sun gaza cika alkawurran da suka dauka bisa ga dalilai na rashin fitowar al'umma yayin zaben wajen dangwala kuri'u.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel