Barkiya na APC ya samu kuri’a 340, 000 a zaben Sanatan Katsina

Barkiya na APC ya samu kuri’a 340, 000 a zaben Sanatan Katsina

- Jam'iyyar APC ce ta ci kujerar Sanata a Yankin Katsina ta tsakiya

-Sakamakon zaben Katsina su na cigaba da shigowa a halin yanzu

Barkiya na APC ya samu kuri’a 340, 000 a zaben Sanatan Katsina
Barkiya ya doke 'Dan takarar PDP a kujerar Sanata a Katsina
Asali: Getty Images

APC ta samu kujerar Sanatan yankin Katsina ta tsakiya inda Injiniya Kabir Barkiya ya doke ‘dan takarar jam’iyyar adawa PDP watau Hamisu Gambo. INEC ta sanar da cewa APC ta samu 340, 8000 inda PDP ta samu kuri’u 124, 372.

Kabir Barkiya wanda tsohon Darektan hukumar nan ta FERMA mai alhakin gyara hanyoyin Najeriya shi ne ya samu wannan gagarumar nasara. Barkiya ya nemi ya ribanya abin da abokin hamayyar sa ya samu har kusan sau 3.

KU KARANTA: Saurayi ya mutu ranar da ya kadawa Buhari kuri’a a Daura

Mun ji cewa Hukumar zabe na INEC mai zaman kan-ta ce ta sanar da zaben ta bakin Farfesa Adebayo Hamzat wanda shi ne jami’in da ya tattara kuri’un da su ka fito daga kananan hukumomi 11 na cikin mazabar jihar ta Katsina.

Akwai masu zabe fiye da miliyan guda a yankin, sai dai mutane 495, 351 kadai aka tantance a zaben da aka yi a karshen makon da ya gabata. Daga cikin wadannan jama’a kuma mutum 485, 254 ne kuri’ar su tayi tasiri a wannan zabe.

Kabir Barkiya ya doke Sanata mai-ci watau Umaru Kurfi ne a zaben fitar da gwani na jam’iyyar APC da aka yi kwanakin baya. Abdulaziz Yaradua da Ibrahim Ida su na cikin wadanda su ka nemi kujerar na Sanatan Katsina ta tsakiya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng