Da dumin sa: Ma’aikatan INEC biyu sun gudu da sakamakon zabe a Katsina

Da dumin sa: Ma’aikatan INEC biyu sun gudu da sakamakon zabe a Katsina

Wasu ma’aikatan hukumar zabe ta kasa (INEC) na wucin gadi sun arce da sakamakon zabe a wasu mazabu biyu a Katsina.

Lamari na farko ya faru ne a akwati ta 004 a mazabar Wakilin Yamma III a karamar hukumar Katsina, yayin da lamari na biyu ya faru, yayin da na biyu ya faru a mazabar Wakilin Yamma II.

A mazabar wakilin Yamma III, ma’aikacin ya gudu ne da takardar sakamakon zaben shugaban kasa yayin da a mazabar Wakilin Yamma II, ma’ikacin ya gudu ne da takardar sakamakon zaben majalisar wakilai.

INEC ta shaida wa majiyar mu cewar ta yi iya bakin kokarin ta domin samo ma’aikacin da ya tsere da takardar sakamakon amma hakan bai yiwu ba.

Da dumin sa: Ma’aikatan INEC biyu sun gudu da sakamakon zabe a Katsina
Shugaban INEC; Farfesa Mahmoud Yakubu
Asali: UGC

Mun karbi sakamako na akwati 25, mu na jirn dayan, na akwati 004,” a cewar jami’in INEC.

DUBA WANNAN: Zabe: Sakamako daga jihohin Sokoto, Kebbi da Jigawa

Ba mu san inda ma’aikacin ya gudu da sakamakon zaben ba. Mun shafe fiye da sa’o’i biyar mu na kiran sa a waya amma ya ki amsa wa. Wakilan jam’iyya da jami’an tsaro sun yi neme shi amma babu wanda ya gan shi har yanzu. Haka mu ka hakura, tilas mu soke sakamakon akwatin,” jami’in ya kara da cewa.

Kazalika, mai tattara sakamakon mazabar Wakilin Yamma II ya ce babu takrdun sakamakon akwati biyu daga cikin sakamakon zabe na mazabar sa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel