An kama muggan makamai da mota cike da kwayoyi a Kano, hotuna

An kama muggan makamai da mota cike da kwayoyi a Kano, hotuna

Rundunr ‘yan sandan Najeriya reshen jihar Kano ta sanar da cewar ta yi nasarar kama wani mutum da wukake kimanin 6750 a Kwanar Dumawa da ke hanyar zuwa jihar Katsina da kuma ma su safarar kwayoyi da kayan maye.

Rundunar ta ce mutumin da aka wukaken ya na kan hanyar sa ne ta shiga da su jihar Katsina.

M. I. Wakili, Sabon Kwamishnan ‘yan sanda da aka kawo jihar Kano daga Katsina, ya ce su na gudanar da bincike a kan wukaken da kuma mutumin da su ka kama kafin daukan mataki na gaba.

Kazalika, kwamishinan ya bayyana cewar jami’an ‘yan sanda sun yi nasarar kama wani mutum da madarar sukudayin mai yawan gaske.

Kwamishina Wakili ya kara da cewa sun kara kama wata motar dakon kaya da aka makare ta miyagun kwayoyi kuma aka shigo da ita jihar Kano.

An kama muggan makamai da mota cike da kwayoyi a Kano, hotuna
Mota dauke da durorukan madarar sukadayin
Asali: Facebook

An kama muggan makamai da mota cike da kwayoyi a Kano, hotuna
Kwayoyin da aka kama a babbar motar dako
Asali: Facebook

An kama muggan makamai da mota cike da kwayoyi a Kano, hotuna
Wukake
Asali: Facebook

An kama muggan makamai da mota cike da kwayoyi a Kano, hotuna
An kama muggan makamai da kwayoyi a Kano
Asali: Facebook

A wata hira da aka yi da shi bayan ya karbi aiki a jihar Kano, Kwamishina Wakili ya ce ana sayar da kwaya a jihar Kano kamar yadda ake sayar da goro, tamkar babu dokar da ta hana tu’ammali da miyagun kwayoyi.

Ko a cikin satin nan saida rundunar ‘yan sanda a jihar Kano ta sanar da cewa ta kama ‘yan dabar siyasa 500 kuma ta kara da cewa za ta gurfanar da su a gaban kotu.

DUBA WANNAN: Babbar Magana: ‘Yan daba sun kai wa tawagar Osinabjo hari a Ilorin

Sai dai a yayin da rundunar ‘yan sandan ke kokarin shawo kan aiyukan bangar siyasa a jihar Kano, sai gashi a yau din nan an samu rahoton barkewar wani kazamin rikici yayin kamfen din jam’iyyar PDP karkashin jagorancin madugun kwankwasiyya, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, a karamar hukumar Bebeji.

Rahotanni sun bayyana cewar an yi asarar rayuka da dukiyoyi yayin rikicin.

Rikicin ya yi tsamarin da ta kai ga wasu fusatattun matasa da ake zargin magoya bayan jam’iyyar PDP ne sun saka wa gidan mamba a jam’iyyar APC, dan majalisar tarayya mai wakiltar Kiru da Bebeji a majalisar wakilai, Abdulmumin Jibrin Kofa, wuta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel