An bude jami’ar Sojoji da sama da dalibai 1000 a jahar Borno
Sabuwar jami’ar Soji da aka bude a garin Biu na jahar Borno ta fara aiki, inda ta dauki dalibai dubu daya da goma sha shiga a karon farko na zangon karatun 2018/2019, kamar yadda rahoton kamfanin dillancin labaru, NAN, ta tabbatar.
Mataimakin shugaban jami’ar, Farfesa David Malgwi ya bayyana cewa sun dauki daliban ne bisa kyakkyawar sakamakon da suka samu a jarabawar shiga makarantun gaba da sakandari na JAMB.
KU KARANTA: Wani matashi ya aika da abokinsa barzahu sakamakon cacar baki akan siyasar Kano
Majiyar Legit.ng ta ruwaito Malgwi yana fadin sun dauki dalibai dari biyu da biyu, 202 a tsangayar karatun kwamfuta, dari da tamanin, 180 a tsangayar kimiyya da fasaha, dari da hudu,104 a tsangayar kula da muhalli, dari uku da sittin da tara, 369 a bangaren gudanarwa da kuma 161 a tsangayar ilimin kimiyya.
Haka zalika Malgwi yace sun dauki wasu rukunin dalibai dubu daya da zasu yi a karatu a karkashin tsarin sharan fage na shiga jami’ar, wanda ake kira “Remedials” a turance. Daga nan yayi kira ga kafatanin daliban dasu kaurace ma miyagun ayyuka da makamantansu.
Sa’annan ya tabbatar musu da cewa hukumar jami’ar ta dauki kwararan matakai don tabbatar da tsaron lafiya da dukiyoyin dalibai da ma’aikatan jami’ar, da ma na al’ummar garin Biu gaba daya, don haka yayi kira a garesu dasu kasance masu lura, ankara da takatsantsa.
Wakilin babban hafsan sojan kasa, Laftanar Tukur Yusuf Buratai, Manjo Janar Chukwuemeka Okwankwo ya yaba ma ministan Ilimi, Adamu Adamu tare da jinjina masa bisa goyon bayan daya bayar wajen kafa wannan jami’a.
Daga karshe yayi kira ga sabbin daliban dasu kasance masu bin doka da ka’ida, sa’annan kada su kasance masu zaman banza da zaman kashe wando, su tabbata sun bada gudunmuwa domin cigaban al’umma.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng