Gwamnatin Najeriya ta dawo da Jakadanta dake kasar Saudiyya don amsa tambayoyi

Gwamnatin Najeriya ta dawo da Jakadanta dake kasar Saudiyya don amsa tambayoyi

Ma’aikatar kula da harkokin kasashen waje ta Najeriya ta gayyaci Jakadan Najeriya a kasar Saudiyya, Jakada Muhammadu Yunusa daya gurfana a gaban ministan harkokin kasashen waje, Geoffrey Onyeama biyo bayan kararsa da gwamnatin kasar Saudiyya ta kai ma Buhari.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito gwamnatin kasar Saudiyya a karkashin jagorancin Mai alfarma Sarki Salmanu ta zargi Muhammad Yunusa da laifin rashin bata hadin kai a wasu al’amura, kamar yadda babban sakataren ma’aikatar ya bayyana.

KU KARANTA: Osinbajo ya yi kira ga Hausawan Legas su zabi Buhari don cigaba da morewa

Babban sakataren ma’aikatar harkokin kasashen waje na Najeriya, Jakada Mustapha Sulaiman ne ya bayyana haka cikin wasikar gayyatar da ya aike ma Jakada Muhammad Yunusa, inda yake shaida masa korafin da masarautar Saudi ke dashi akansa.

Babban sakataren ya bayyana cewa ma’aikatar ta gayyaci Yunusa ne domin bada amsoshi ga game da tuhumar da gwamnatin kasar Saudiyya tayi masa, tare da jin nasa bangaren kafin daukan wani mataki.

“Gwamnatin kasar Saudiyya na zarginga da kin bata hadin kai, wanda hakan zai kawo sabani ga kyakkyawar dangantakar dake tsakanin kasashen biyu, aminan juna. Don haka a madadin minista, ina gayyatarka ka dawo gida domin tuntuba, da gaggawa.

“Hakan ya zama wajibi domin mu samu amsoshin da zaka bayar game da tuhume tuhumen da gwamnatin Saudiyya ta yi maka akan rashin bata hadin kai wanda hakan ka iya lalata kyakkyawar alakar dake tsakanin Najeriya da Saudi Arabia.

“Don haka ka mika ragamar iko a ofishin jakadancin Najeriya dake Saudiyya ga babban jami’I mafi girma a ofishin, ka yi gaggawar dawowa Najeriya domin amsa tambayoyi.” Inji wasikar da babban sakataren ya rattafa ma hannu a ranar 18 ga watan Feburairu.

Dama dai jama’a da dama sun dade suna korafi akan kamun ludayin Muhammad Yunusa, musamman ma yan Najeriya mazauna kasar Saudiyya, inda ko a kwanakin baya ma sai da aka jiyo Yunusan yana musayar yawu da Sheikh Ahmad Abubakar Mahmud Gumi akan daukan mata masu sanye da nikabi fasfo.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel