Sabuwa: Adadin Fulanin da aka kashe a Kajuru ya haura 130 - El-Rufa'i ga Buhari

Sabuwa: Adadin Fulanin da aka kashe a Kajuru ya haura 130 - El-Rufa'i ga Buhari

A ranan Talata, Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa'i ya bayyana cewa adadin yan jama'ar Fulain da aka hallaka a karamar hukumar Kajuru, kudancin jihar Kaduna sun haura 130.

A ranan Juma'ar da ta gabata, gwamna El-Rufa'i ya sanar da cewa mutane 66 ne suka rasa rayukansu a garin.

Ya yi wannan jawabi ga manema labaran fadar shugaban kasa bayan ganawarsu da shugaba Buhari a Aso Villa, birnin tarayya Abuja.

An yi ganawar ne kan karuwar rashin tsaro a jihar Kaduna, Borno, Yobe da Adamawa a kwanakin nan.

Kungiyar kiristocin Najeriya ta karyata rahoton gwamna El-Rufa'i cewa Fulani 66 aka kashe a jihar, amma gwamnan ya siffantasu a matsayin marasa hankali.

KU KARANTA: EFCC da damke lauyan Atiku kan badakalar $2m

Yace a matsayinsa na gwamna, yana samun rahotoanni da jami'an tsaro kullun da safe kuma akansu yake aiki. Rahoton da ya smau yanzu shine mutanen da aka kashe sun haura 130, ba ma 66 ba.

Ya kara da cewa iyalan wadanda aka kashe sun baiwa gwamnatin jihar sunayen wadanda aka kashe kuma za'a saki ba da dadewa.

Kwamishanan yan sandan jihar, Ahmad AbdulRahman, wanda ya halarci taron tsaron yace an damke mutane takwas game da wannan kisan gillan.

Mun kawo muku cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya shiga ganawar gaggawa da manyan hafsoshi tsaron Najeriya, sifeton yan sanda, Mohammed Adamu, da wasu gwamnonin arewacin Najeriya a ranan Talata, 19 ga watan Febrairu, 2019.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel