MBS na kasar Saudiyya ya warware zare da abawa a kan rahoton sayen Manchester
Yarima mai jiran gadon sarautar kasar Saudiyya, Mohammed Bin Salma da ake wa lakabi da ‘MBS’, ya musanta rahotanni da ke yawo a kafafen yada labarai a kan cewar yana shirin kasha kudin kasar Ingila Yuro 3.8bn domin sayen kungiyar kwallon kafa ta Manchester United.
An fara yada jita-jitar cewar Yarima MBS na son sayen kungiyar kwallon kafa ta Machester da ke kasar Ingila a watan Oktoba na shekarar 2018.
Sabuwar jita-jitar sayen kungiyar kwallon kafar ya kara bulla a kafafen yada labarai da sada zumunta a karshen makon jiya.
Kafafen yada labarai da dama sun rawaito cewar Yarima MBS na shirin sayen kungiyar Man. United a kan zunzurutun kudin kasar Ingila da yawan su ya kai Yuro biliyan 3.8.
Tun a watan Mayu na shekarar 2005 wasu ‘yan kasuwa ‘yan asalin kasar Amurka su ka mallaki hannun jari ma fi rinjaye na kungiyar Manchester United a kan kudin kasar Ingila Yuro miliyan 790.
Turki Al-shabanah, kakakin Yarima MBS ya tabbatar da cewar babu gaskiya a cikin rahotannin da ke bayyana cewar mai gidan na san a shirin sayen kungiyar kwallon kafa ta Manchester United.
DUBA WANNAN: Zabe: ‘Yan sanda sun kama wani mutum da kuri’un bogi a Sokoto
A cewar Al-shabanah; “babu gaskiya a cikin rahotannin da ke danganta Yarima MBS da niyyar sayen kungiyar kwallon kafa ta Manchester United.
Sannan ya kara da cewa; “kungiyar Manchester United ta gudanar da wani taro domin kafa wani asusun tsimi da tanadi domin ma su sha’awar saka hannun jari su zuba kudi da za a ke amfani da su wajen gudanar da harkokin kungiyar sannan a raba riba tare da su. A kan wannan maganar aka tsaya kuma har yanzu ba a cimma wata matsaya ba.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng