Operation Sharan Daji: Sojoji sun ceto mutum 80 da akayi garkuwa da su a Zamfara

Operation Sharan Daji: Sojoji sun ceto mutum 80 da akayi garkuwa da su a Zamfara

Sashi Sojojin Sama na Operation Sharan Daji da ke yaki da 'yan bindiga a yankin Arewa maso Yamma ya ce dakarun soji sunyi nasarar ceto mutane 80 da akayi garkuwa da su bayan wani sumame da sojin suka kai a kusa da Dajin Dumburum na jihar Zamfara.

Wannan sakon ta fito ne daga bakin kakakin rundunar na wucin gadi, Manjo Clement Abiade yayin sanarwa da ya fitar a Zamfara.

Ya ce an kai sumamen ne a makon da ta gabata inda sojojin saman su kayi hadin gwiwa da sojojin kasa da suka datse hanyoyin da 'yan bindigan za su bi su tsere.

DUBA WANNAN: Jiga-jigan 'yan siyasar Najeriya da ba su taba sauya sheka ba

Sojoji sun ceto mutum 80 da akayi garkuwa da su a Zamfara
Sojoji sun ceto mutum 80 da akayi garkuwa da su a Zamfara
Asali: Twitter

Kakakin sojin ya ce anyi nasarar damke mutane shida da ake kyautata zaton masu garkuwa da mutane da satar shanu ne kuma an kwato dabobin da aka sace, bindigu da wasu makamai.

Ya ce za a mika wadanda aka kama a hannun jami'an 'yan sanda domin a zurfafa bincike kana a gurfanar da su gaban kuliya.

Sai dai ya kuma ce rundunar sojin tayi rashin dakarunta shida da suka riga mu gidan gaskiya musayar wuta da su kayi da 'yan bindiga a garin Bini da ke kusa da karamar hukumar Maru.

Ya kara da cewa rundunar ba za tayi kasa a gwiwa ba wurin cigaba da sauke nauyin da ya rataya a kanta na magance 'yan bindigan na jihar Zamfara.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel