Buhari ya nesanta kansa daga furucin El-Rufai kan duk wanda yayi katsalandar a zaben kasar

Buhari ya nesanta kansa daga furucin El-Rufai kan duk wanda yayi katsalandar a zaben kasar

- Buhari ya yi kira ga mutanen Najeriya da ma na kasar waje da su yi watsi da duk kalaman da wani ya yi na batanci game da ayyukan masu sa-ido a zabe

- Ya basu tabbacin samun ingantaccen tsaro tare da yin zabe cikin lumana

- Ana kallon hakan a matsayin raddi ka furucin da El-Rufai yayi a kwanakin baya

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi kira ga mutanen Najeriya da ma na kasar waje da su yi watsi da duk kalaman da wani ya yi na batanci game da ayyukan masu sa-ido a zabe ko kuma kasashen su cewa ba da yawun gwamnati ya yi ba.

Buhari yace a matsayin sa na shugaban Najeriya burin sa shine ya ga ana zaman lafiya a kasa da kuma karrama baki da suka shigo kasar gami da ba su kariya, amma ba Abinda zai tada musu da hankali ba.

Buhari ya nesanta kansa daga furucin El-Rufai kan duk wanda yayi katsalandar a zaben kasar

Buhari ya nesanta kansa daga furucin El-Rufai kan duk wanda yayi katsalandar a zaben kasar
Source: Depositphotos

Duk da cewa shugaban kasar bai ambaci sunan wani ba ana dai ganin Gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, ne a kwanakin baya ya bayyana cewa duk wanda ya zo kasar yayi kokarin yin katsalandan a al’amurran kasar nan za a koma da gawar sa ne kasar sa.

KU KARANTA KUMA: Babu wani jami’in gwamnati da ba a zarga da rashawa ba - Atiku

Shugaba Buhari da ya fadi haka a jawabi da yayi wa ‘yan Najeriya ranar Alhamis, 14 ga watan Fabrairu ya kuma yi kira ga ‘yan Najeriya da su kwantar da hankalun su sannan a fito a yi zabe lafiya.

Bayannan ya tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa gwamnatin sa za ta zuba ido ta ga cewa an gudanar da zabukkan dake tafe cikin kwanciyar hankali da lumana.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel