Adam Zango ya yi karin haske a kan kai masa farmaki saboda zagin Buhari

Adam Zango ya yi karin haske a kan kai masa farmaki saboda zagin Buhari

- Jarumin Kannywood, Adam A. Zango karyata labarin da ke yaduwa a kafafen sada zumunta na cewa matasan Kano sun masa jina-jina bayan ya zagi shugaba Buhari

- Zango wanda ake yiwa lakabi da Fresh Prince ya ce matasa ba su doke shi ba kuma bai zagi Shugaba Buhari ba duk da cewa Atiku Abubakar ya ke goyon baya

- Jarumin fim din ya ce hoton da ake yadawa an samo shi ne daga fim din 'Basaja Gidan Yari' da ya yi a shekarar 2015

Fitaccen jarumin Kannywood kuma mawaki, Adam A. Zango ya karyata cewa wai wasu fusatattun matasa sunyi masa duka a garin Kano domin ya 'zagi' Shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Wasu mutane sun rika yadawa a kafafen sada zumunta a ranar Alhamis cewa an kwantar da Zango a asibiti bayan wasu 'yan daba sun lakada masa duka saboda ya fice daga cikin jerin magoya bayan shugaba Muhammadu Buhari ya koma goyon bayan dan takarar shugabancin kasa na PDP, Atiku Abubakar.

DUBA WANNAN: Kano: An kama buhu 14 makare da kuri'u da aka dangwale

Adam Zango ya yi karin haske a kan kai masa farmaki saboda zagin Buhari
Adam Zango ya yi karin haske a kan kai masa farmaki saboda zagin Buhari
Asali: Facebook

An rika yada wani hoton jarumin sanye da riga da jini a kansa da jikinsa inda akayi ikirarin cewa fusattun matasa ne suka yi masa duka a Kano bayan ya furta kalaman batanci a kan Shugaba Buhari.

Sai dai Zango wanda ake yiwa lakabi da Fresh Prince ya shaidawa Daily Trust cewa babu kanshin gaskiya a cikin labarin da ke yaduwa a kafafen sada zumunta a ranar Alhamis.

Ya ce: "Babu kanshin gaskiya a cikin labarin da ke yaduwa a kafafen sada zumunta; Maganan gaskiya itace matasa ba suyi min duka ba kuma ban zagi Shugaba Buhari ba."

"Hoton da ake yadawa tare da jita-jitar an dauke shi ne a 2015 yayin da ake shirin fim din 'Basaja Gidan Yari', a cikin fim din na fito a Jabir wanda ke yaudarar wadanda suka taro kudinsa ta hanyar haram," inji shi.

Zango ya yi kira da al'umma suyi watsi da labarin domin yana cikin koshin lafiya kuma yana cigaba da yiwa Atiku Abubakar yakin neman zabe domin ya yi nasarar zama Shugaban kasar Najeriya a gobe.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164