Zaben: Oshiomhole ya roki INEC ta amince da 'yan takarar jihar Zamfara

Zaben: Oshiomhole ya roki INEC ta amince da 'yan takarar jihar Zamfara

Shugaban jam'iyyar APC na kasa, Adams Oshiomhole ya bukaci Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta INEC ta amince da 'yan takarar jam'iyyar APC reshen jihar Zamfara su fafata a babban zaben da ke tafe.

A wasikar da ya aike wa hukumar a ranar 13 ga watan Fabrairu, Oshiomhole ya ce hukuncinnda kotun daukaka kara ta yanke a Sokoto ya bawa jam'iyyar damar fitar da 'yan takara a jihar na Zamfara.

A wasikar mai lamba APC/NIDQ/INEC/19/019/08, shugaban jam'iyyar ya bukaci INEC tayi biyaya ga umurnin kotu cikin gaggawa.

Zaben: Oshiomhole ya roki INEC ta amince da 'yan takarar jihar Zamfara

Zaben: Oshiomhole ya roki INEC ta amince da 'yan takarar jihar Zamfara
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Zabe: 'Yan takara 10 sun janye goyon bayan su ga Bindow

A wata wasikar daban, Attorney Janar na kasa, Abubakar Malami ya bukaci INEC ta dage zaben jihar Zamfara saboda shari'ar da har yanzu ake yi game da hallarcin bawa APC damar fitar da 'yan takara.

"Kamar yadda muka bayyana a wasikar mu ta baya na ranar 25 ga watan Janairun 2019 dangane 'yan takarar jam'iyyar mu na Gwamna, Mataimakin Gwamna, 'Yan Majalisun Tarayya da na Jiha a zaben 2019.

"Muna son su sanar da ku cewa kotun daukaka kara na jihar Sokoto tayi watsi da daukaka kara da aka shigar a kan hukuncin da kotu ta yanke a ranar 25 ga watab Janairun 2019.

"Muna fatan za ku dauki mataki a kan lamarin cikin gaggawa.

"Cikin wasikar akwai kofi na umurnin da kotu ta yanke a ranar 13 ga watan Fabrairun 2019."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel