Fitaccen jarumin fina-finan Hausa ya gargadi ‘yan Najeriya a kan zabe

Fitaccen jarumin fina-finan Hausa ya gargadi ‘yan Najeriya a kan zabe

Fitaccen jarumin masana’antr shirya fina-finan Hausa (Kannywood), Abba El-Mustapha, ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su san cewar akwai rayuwa bayan zabe, don haka kar su bari siyasa ta raba kan su.

El-Mustapha, wanda aka fi sani da ‘Abba Ruda’ ya yi wannan jan hankali ne a wani rubutaccen sako da ya fitar a shafin sa na sada zumunta (Instagram) yayin hutun krshen mako.

Kada ka bari siyasa ta had aka rigima da kowa. Ka yi siyasa cikin mutunci da girmama wa don akwai rayuwa bayan zabe,” a cewar jarumin.

Jarumin ya kara yin kira ga ‘yan Najeriya a kan su daina dage wa a kan lallai sai an bi ra’ayin sun a siyasa domin kowa da nasa ra’ayin.

Fitaccen jarumin fina-finan Hausa ya gargadi ‘yan Najeriya a kan zabe
Abba Ruda
Asali: Twitter

Kar ka tursasa wa kowa bin ra’ayin ka, kowa yana da nasa. Idan ka girmama ra’ayin wani, kai ma sai a girmama na ka. Banga da ta’addancin siyasa bas u dace ga duk wani mutum mai hankali ba,” a cewar Abba Ruda.

DUBA WANNAN: Rashin jituwa: Shekarau ya yi karin haske a kan alakar sa da Buhari

Sannan ya yi kira ga matasa da su bari ‘yan siyasa na amfani da su domin tayar da husuma da tarzoma a lokutan yakin neman zabe da lokacin zabe da ma bayan sa.

Ku daina bari ‘yan siyasa su na amfani da ku wajen tayar da rigima a cikin al’umma. Ba don cigaban kasa su ke amfani da ku ba, su na amfani da ku ne domin biyn bukatr kan su. Allah ya ganar da mu, ya sa mu dace,” in ji jarumi Abba Ruda.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng