Babbar kotu ta garkame shugaban bankin Ecobank akan satar naira miliyan 411
Wata babbar kotun tarayya dake zamanta a garin Ikoyi na jahar Legas ta bada umarnin daure manajan bankin Ecobank, Ifeanyi Chukwu Azike sakamakon tuhumar da aka gabatar mata akansa daya dangancin damfarar wani abokin huldar bankin, tare da sace masa zambar kudi naira miliyan dari hudu da goma sha daya.
Majiyar Legit.ng ta ruwaito sashin yaki da damfara ta rundunar Yansandan Najeriya ce ta gurfanar da Azike gaban Alkali mai sharia Ayotunde Faji a ranar Talata, 12 ga watan Feburairu akan tuhume tuhume guda uku da suka hada da zamba, damfara da kuma yaudara.
KU KARANTA: 2019: El-Rufai ya bayyana manyan dalilai guda 4 kwarara da zasu kayar da Atiku
Dansanda mai shigar da kara ya bayyana ma kotu cewa a tsakanin shekarar 2016 zuwa 2017 Azike ya damfari wani abokin huldar bankin Ecobank, Okafor Ikenna kudi naira miliyan 150, da sunan zai saya masa hannun jarin gwamnatin tarayya.
Haka zalika yayi amfani da alamar sa hannun Ikenna, wanda ya rattafa da kansa wajen bude wani sabon asusun banki da sunan Ikenna Okafor Kelvin mai lamba 5333063028, wanda da ita yayi amfani wajen kwashe zambar kudi N411,000,000 mallakin Ikenna.
Don haka Dansanda mai shigar da kara Daniel Apochi ya bayyana ma kotu cewa laifin da ake tuhumar Azike dasu sun saba ma sashi na 1(1)(a), 15(1)(2) da na 15(2) na dokokin yaki da zamba cikin aminci da damfara.
Sai dai bayan zayyana masa dukkanin tuhume tuhumen dake kansa, sai Azike ya barar dasu gaba daya, inda ya musanta aikata dukansu, daga nan ne Alkali Faji ya bada umarnin a daure masa shi a gidan yari, sa’annan ya dage sauraron karar zuwa ranar 8 ga watan Maris.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng