Siyasar Kano: An kone ofishin kamfen din dan takarar gwamna a PDP

Siyasar Kano: An kone ofishin kamfen din dan takarar gwamna a PDP

Wasu ‘yan dabar siyasa da ake zargin na yi wa jam’iyyar APC aiki sun saka wa ofishin yakin neman zaben dan takarar gwamnan Kano a karkashin inuwar jam’iyyar PDP, Abba Kabir Yusuf, wuta.

A wani jawabi da Sanusi Dawakin Tofa, kakakin dan takarar na PDP, ya fitar y ace lamarin ya faru ne ranar Lahadi, lokacin da ake gudanar da taron kamfen din dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar.

Dawakin Tofa ya ce an tabbatar da cewar wadanda su ka ka kone ofishin, mambobin jam’iyyar APC ne.

Siyasar Kano: An kone ofishin kamfen din dan takarar gwamna a PDP

Siyasar Kano: An kone ofishin kamfen din dan takarar gwamna a PDP
Source: Facebook

Kakakin dan takarar ya ce su na zargin wani Junaidu Abdulhamid, mataimaki na musamman ga shugaban jam’iyyar APC na jihar Kano, Abdullahi Abbas, da jagorantar ‘yan daba fiye da 60 wajen kone gidan mai lamba 36 da aka mayar ofishin siyasa a unguwar Chiranchi da ke karamar hukumar Gwale.

DUBA WANNAN: Farmakin gidan Abdullahi Abbas: Rundunar ‘yan sanda ta kama ‘yan daba 28 a Kano

Sun kone gidan kurmus tare da lalata wata mota kirar Golf III mai lamba kamar haka; NSR 237 AE.

“Shaidar gani da ido ya tabbatar ma na da cewar wadanda su ka kona gidan, su ne su ka kai wa magoya bayan kwankwasiyya hari a kofar yayin hawan Daushe lokacin bikin sallah a Kano,” a cewar Dawakin Tofa.

Kazalika, ya zargi gwamnatin jihar Kano da yin amfani da ‘yan daba da ke dauke da muggan makamai yayin taron kamfen da gangamin jam’iyyar APC a Kano.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel