Oshiomhole, Amaechi, Aregbesola sun sha ruwan duwatsu, Tinubu ya sabe da wayo - Gwamna Amosun

Oshiomhole, Amaechi, Aregbesola sun sha ruwan duwatsu, Tinubu ya sabe da wayo - Gwamna Amosun

Shugaban jam'iyyar All Progressives Congress, Mr Adams Oshiomhole, minista Sufuri, Rotimi Amaechi da tsohon gwaman jihar Osun, Rauf Aregbesola, sun sha ihu da ruwan duwastu a taron yakin neman zaben shugaban kasa a ranan Litinin, 11 ga watan Febrairu, 2019 a jihar Ogun.

Rikicin ya fara ne yayinda shugaba APC, Adams Oshiomole, ya ambaci sunan dan takaran gwamnan jihar Ogun, Dapo Abiodun, yayin gabatar da jawabinsa.

Da rikicin ya cigaba, sai da gwamnan jihar Ibikunle Amosun ya kwantar da kuran inda ya yayi magan ga mutanen cewa suyi hakuri kuma su girmama shugaba Muhammadu Buhari.

Duk da hakan, kurar bata kwanta ba har sai lokacin da Oshiomole ya hakura ya koma kujerarsa sannan mataimakin shugaban kasa, Yem Osinbajo, ya tashi ya gabatar da nasa jawabinsa.

KU KARANTA: Sabuwa: Yadda ake sayar da gyada akan titi ake sayar da 'kwaya' a Kano - Sabon Kwamishanan jihar Kano, Ali Wakili

Gwamnan jihar, Ibikunle Amosun ya bayyana cewa: "Rikicin da ya mamaye jam'iyyar APC a jihar Ogun ya sake hurowa wuta a yau (Litinin) yayinda mambobin jam'iyyar suka yiwa shugaban jam'iyyar APC ta kasa, Adams Oshiomole; tsohon gwamnan jihar Osun, Rauf Aregbesola; da diraktan kamfen Buhari, Rotimi Amaechi, ihu da kuma jifansu.

A karo na farko, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, bai yi jawabi a taron yakin neman zaben APC ba kuma ya sabe da wayo daga farfajiyar taron yayinda Buhari ke gabatar da jawabi."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel