Kuna kiran masoyanku su sosu don Allah, kuna sonsu don kudi – Naziru ga A Zango
Shahararren mawakin nan daga yankin Arewacin Najeriya, kuma sarkin wakar sarkin Kano, Naziru Ahmad ya mayar da martani ga abokin aikinsa, Adam A Zango, bisa matakin daya dauka na sauya sheka daga gidan siyasar Buhari zuwa gidan siyasar Atiku Abubakar.
Majiyar Legit.ng ta ruwaito wata majiya dake kusa da Zango ce ta tabbatar da haka, inda majiyar tace Zango ya yanke shawarar jefar da kwallon mangwaro domin ya huta da kuda ne bayan wata ganawar sirri da yayi da wasu makusanta Atiku Abubakar.
KU KARANTA: Siyasa rigar yanci: Adam Zango ya yi fatali da Buhari, ya koma gidan Atiku a guje
Zango ya yi wannan ganawa da makusanta Atikun ne da kuma wasu shuwagabanannin jam’iyyar PDP ne a ranar Laraba, 6 ga watan Feburairu a babban birnin tarayya Abuja, yayin da yake kan hanyarsa ta zuwa Kaduna.
Sai dai Naziru ya yi masa raddi, inda yayi mamakin yadda a baya Zango ya yi kira ga masoyansa dasu goyi bayan Buhari saboda Allah, amma sai ga shi ta bayyan ashe saboda kudi shi kuma yake son Buharin, don haka yayi kira ga yan Fim dasu daina raina hankalin masoyansu.
“Kun zama kamar gyada, wannan ya damka yayi taraba wannan ya damka yayi taraba, wannan ya damka yayi kaduna, bah aka ake yi ba, ka kira mutane kar su sayar da yancinsu, kar su sayar da kuri’arsu, kace ko za’a kasheka sai Buhari, yan tun a kasheka ka ji yar matsa kawai ka hakura.
“Kunce ayi Buhari, meye dalili? Aikin da yayi, toh yau aikin da Buhari ya goge ne? ba kyau, kuma cutan mabiyanku, kuna cewa su zo suyi don Allah, ku kuna yi don kudi, saboda ba’a baka kudi ba kawai shikenan lissafinka sai ya kare?
“Ba haka ake yi ba, duk abinda zaka yi da mutum yi da shi don Allah, suna sonku don Allah, kuma ku dinga makancewa kuna jansu, masoyinka ba abin wasa bane……..” Inji Naziru.
Idan za’a tuna, masana’antar Kannywood ta rabu gida biyu tsakanin magoya bayan Buhari, da kuma magoya bayan Atiku Abubakar, inda a ko a makon daya gabata sai da aka ji Ummi Zee Zee da Zaharaddeen Sani suna cacar baki akan kudin da Atiku ya basu.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng